Sarkin Hausawan Kalaba ya fusata kan yage hotunan ’yan Boko Haram da ake nema
Sarkin Hausawan Kalaba, Alhaji Salisu Abba Lawal ya nuna matukar damuwarsa kan abin da wani da ba a san kowane ne ba ya aikata, na yage jerin hotunan ’yan kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, da aka kafa a kofar ofishinsa.Sarkin ya nuna rashin jin dadinsa a hirarsu da Aminiya, ya ya […]
Sarkin Hausawan Kalaba, Alhaji Salisu Abba Lawal ya nuna matukar damuwarsa kan abin da wani da ba a san kowane ne ba ya aikata, na yage jerin hotunan ’yan kungiyar Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, da aka kafa a kofar ofishinsa.
Sarkin ya nuna rashin jin dadinsa a hirarsu da Aminiya, ya ya kira duk wanda ya yaga takardar hotunan da cewa mara kishin kasa ne. Ya ce duk mutumin da ya aikata haka, ya nuna wa duniya cewa shi ba mai gaskiya ba ne: “kila ma yana daya daga cikin wadanda hotonsa ke jiki, yake bin dare ya yaga, don gudun kada a gane shi, asirinsa ya tonu.”
Daga nan ya bayyana cewa hukuma da ta ba shi fastar aka lika, ya kai mata rahoton abin da ya faru kuma sun ce za su kara kawo masa wata a sake likawa.
Wakilinmu ya lura cewa a duk wuraren da jama’a ke yawan dabdala a Jihar Kurosriba, an kai wannna takarda an lika da nufin za a yi katarin kama masu laifin.