Sarkin Hausawan Kalaba ya musanta ba matashin da ya yi kisan kai kariya

Sarkin Hausawan Kalaba, Alhaji Salisu Abba Lawal ya karyata jita-jitar da ake bazawa cewa shi da Alhaji Nasiru Ishaka, Shugaban kungiyar ’Yan Nijar Mazauna Kurosriba Najeriya na kokarin hada baki da jami’an ’yan sanda a yi kumbiya-kumbiya wajen kin kai Muhammad Abdu, matashin da ya kashe wani dan Nijar makon da ya gabata ta hanyar […]

Sarkin Hausawan Kalaba ya musanta ba matashin da ya yi kisan kai kariya
Sarkin Hausawan Kalaba ya musanta ba matashin da ya yi kisan kai kariya

Sarkin Hausawan Kalaba, Alhaji Salisu Abba Lawal ya karyata jita-jitar da ake bazawa cewa shi da Alhaji Nasiru Ishaka, Shugaban kungiyar ’Yan Nijar Mazauna Kurosriba Najeriya na kokarin hada baki da jami’an ’yan sanda a yi kumbiya-kumbiya wajen kin kai Muhammad Abdu, matashin da ya kashe wani dan Nijar makon da ya gabata ta hanyar daba masa wuka a kirji kotu domin fuskantar shari’a.
Sarkin ya karyata haka tare da shugaban a wata hira mabambanciya da Aminiya a kalaba. Baya ga wannna ma akwai zargin da aka rika yi masu na karbe diyyar wani mamaci da wasu ’yan asalin Kurosriba suka kashe, suka kone gawarsa.
“Gaskiya ba mu ji dadin yadda ake ta zarginmu da haka ba, a matsayinmu na shugabannin al’umma. Yaya za a yi a ce mu yi haka? Wannan karya ce tsagwaronta, babu gaskiya.” Inji Alhaji Abba Lawal, ya kara da cewa: “Mun bar su da Allah, domin babu yadda za a yi a ce ina shugaban jama’a, a ce zan hada baki da wasu a karkata wani hukunci.”
A garin Kalaba, an rika yayata cewa sarkin, shi da shugaban ’yan Nijar, an ba su kudin diyya sun yi rub-da-ciki a kai, sannan kuma sun karbi nagoro don kada a gabatar da hatsabibin matashi, Muhammed Abdu da ke tsare hannun ’yan snada gaban kotu.