Sarkin Hausawan kasar Egba ya nada sababbin hakimai
A ranar Asabar ne, Mai martaba Sarkin Hausawan kasar Egba, a Jihar Ogun, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan, ya nada wasu fitattun mutane 4 a matsayin hakimai. Mutanen da aka nada, aka kuma mika musu takardar shaida, sun hada da Alhaji Nura Isyaku a matsayin Sarkin Fada da Alhaji Aliyu Umar, a matsayin Sarkin Hausawan Alagbado […]

A ranar Asabar ne, Mai martaba Sarkin Hausawan kasar Egba, a Jihar Ogun, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan, ya nada wasu fitattun mutane 4 a matsayin hakimai. Mutanen da aka nada, aka kuma mika musu takardar shaida, sun hada da Alhaji Nura Isyaku a matsayin Sarkin Fada da Alhaji Aliyu Umar, a matsayin Sarkin Hausawan Alagbado da Sarkin Fulanin Abeokuta, Alhaji Bashir Musa Mai Sanduna da wata mata Hajiya Jamila Abdullahi Nasim, wadda aka nada ’Yar Baiwar kasar Egba.
Bikin nadin, wanda aka gudanar a fadar Sarkin Hausawan kasar Egba da ke unguwar Sabo, cikin garin Abeokuta, ya sami halartar wasu wakilan sarakuna Yarbawa da tawagar majalisar Sarakunan Hausawan jihar ta Ogun, karkashin jagorancin shugabanta, Alhaji Umar Muhammed Nalado da kuma wasu manyan mutane daga sassa daban-daban na kasa. Shi ma Alhaji Nasim, mijin Hajiya Jamila, ya jagoranci wasu abokansa ’yan kasar Lebanon domin halartar bikin, wanda ya sami halartar matan aure masu yawa da aka killace musu wurin zama na musamman.
Da yake jawabi, jim kadan bayan nadin, Sarkin Hausawan kasar Egba, Alhaji Ibrahim ya jinjina wa irin gudunmawar hakiman suka bayar wajen cigaban al’ummar Hausawa da kyautata zamantakewarsu da mutanen gari da raya matasa wajen sama musu ayyukan yi da sana’o’i da samar da ilmin addini da na zamani ga kananan yara.
Ya bukaci sauran al’ummar Hausawan sashen su yi koyi da su, musamman ta fannin bayar da gudunmawar da za ta samar da ci gaban jama’a. “Irin rawar da sabon Sarkin Fulani Bashir Mai Sanduna da sabon Sarkin Fada Nura Isyaku suka taka ta fannin samar wa jama’arsu ’yanci da dogaro da kai abin jinjinawa ne. Haka ita ma ’Yar Baiwa Hajiya Jamila, ta yi fice wajen wayar da kan matan aure game da muhimmancin shiga harkokin kasuwanci a cikin gidajensu. Shi kuwa sabon Sarkin Hausawan Alagbado, Alhaji Aliyu Umar, hakurin da ya yi na tsawon shekaru 5 da wucewa ba tare da an tabbatar masa da wannan sarauta ba, saboda wasu dalilai, abin jinjinawa ne,” inji shi.
Shugaban majalisar Sarakunan Hausawan Jihar Ogun, Alhaji Umar Muhammed Nalado da Sarkin Hausawan kasar Awori, Isheri Olofin, Alhaji Muhammad Badamasi, sun yi wa sababbin hakiman matashiya kan amanar da aka damka musu, “Saboda haka sai ku rike ta da tsoron Allah, ku yi gaskiya da adalci tsakanin jama’a”. Inji su.
Sun yi kira ga al’ummar Arewa da ke zaune a wannan sashe da su girmama dokoki, su zauna lafiya da jama’a, wanda shi ne sinadarin cigaba. Haka nan sun bukaci jama’a su rika hanzarta sanar da shugabanninsu bullar duk wani sabon abun da ba a gane masa ba.
Masu kade-kaden Yarbawa da masu busar algaita da mawaka na Hausawa da Fulani tare da maroka sun barje guminsu a bikin.