Sarkin Hausawan Mil 12 da na Agege ba su da lafiya
Sarkin Hausawan yankin Mil 12, Alhaji Usman Jibrin da Sarkin Hausawan Agege, da ke jihar Legas, Alhaji Musa Dogon Kadai suna fama da rashin lafiya. kanin sarkin Hausawan Mil 12, mai suna Abdulhamid Usman ya bayyana cewa sarkin ya dade yana fama da rashin lafiya.‘Sarki ya yi kimanin kwanaki 50 yana fama da rashin lafiya […]
Sarkin Hausawan yankin Mil 12, Alhaji Usman Jibrin da Sarkin Hausawan Agege, da ke jihar Legas, Alhaji Musa Dogon Kadai suna fama da rashin lafiya.
kanin sarkin Hausawan Mil 12, mai suna Abdulhamid Usman ya bayyana cewa sarkin ya dade yana fama da rashin lafiya.
‘Sarki ya yi kimanin kwanaki 50 yana fama da rashin lafiya inda ciwon shanyewar barin jiki ya kama shi. Mun kira likitocinsa da suka zo sai suka ce ciwon da sarki yake fama da shi ba wanda za a yi masa allurai ba ne sai dai a ba shi kwayoyin magani ya sha. Sun ba mu shawarar cewa mu ci gaba da ba shi magunguna kuma mu rika yin addu’a’. Inji shi
Sarkin dogaran sarkin mai suna Adamu ya ce sarkin ya yi kimanin shekaru 90 a duniya kuma shi ne bahaushen da ya fara zama Mil 12.
A bangare daya kuma magatakardar masarautar Hausawan Agege, Alhaji Abubakar Sabo ya tabbatar da rashin lafiyar sarkin Agege Alhaji Musa Dogon kadai.
Alhaji Abubakar Sabo wanda har ila yau shi ne mai unguwar Markaz ya bayyana cewa tuni aka sallamo sarkin Agege daga asibiti.
Ya ce ‘E gaskiya ne sarki yana fama da rashin lafiya. An kwantar da shi a wani asibiti mai da ke Zango amma tuni aka sallame shi yana gida. Mu ne muka bashi shawarar ya zauna a gida ya huta don ya kara murmurewa’.
Sabo ya kara da cewa ‘A zancen da nake yi da kai yana gida yana hutawa kuma yakan fito ya gana da jama’a ya yi hira da su. Yana fama da ciwon hawan jini da ciwon suga amma yana samun sauki kuma muna fata Allah ya bashi lafiya’.
Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Musa Dogon Kadai da na Sarkin Hausawan Mil 12, Alhaji Usman Jibrin suna daga cikin tsofaffin sarakunan Hausawa da suka yi shekara da shekaru suna kan karagar mulki a yankunansu.
Tarihi ya nuna cewa masarautar Hausawan Agege ta fi kowace masarautar Hausawa dadewa ba ma a Jihar Legas ba har da yankin kudu baki daya.