Sarkin Hausawan Samiboda ya nada sababbin hakimai
Mai martaba Sarkin Hausawan Samiboda, Muhammad Faisal Ali ya yi bikin nadin sababbin ‘yan majalisu da hakimai guda 35 a masarautarsa a ranar Asabar din da ta gabata a garin Samiboda da ke dabda Jamhuriyar Benin, a karamar Hukumar Badagry ta Yamma a Jihar Legas.Masarautar za ta samu saukin gudanar da ayyukanta bisa karin hakimai […]
Mai martaba Sarkin Hausawan Samiboda, Muhammad Faisal Ali ya yi bikin nadin sababbin ‘yan majalisu da hakimai guda 35 a masarautarsa a ranar Asabar din da ta gabata a garin Samiboda da ke dabda Jamhuriyar Benin, a karamar Hukumar Badagry ta Yamma a Jihar Legas.
Masarautar za ta samu saukin gudanar da ayyukanta bisa karin hakimai da ‘yan majalisun da ta samu, wadanda a da ba su wuce 16 ba. Sarkin Hausawan na Samiboda ya shaida wa Aminiya cewa, an zabo wadanda aka yi wa nadin ne bisa cancantarsu da kwarewarsu, wanda hakan ya ba shi tabbacin cewa ba za su baiwa marada kunya ba. Ya kuma gargadesu da su ji tsoron Allah, sannan ya yi fatan Allah ya taimake su bisa nauyin da aka daura musu. Kana ya yi kira ga mutanen garin da su bai wa wadanda aka nada goyon baya. Domin a cewarsa bin nagaba, bin Allah ne.
daya daga cikin manyan bakin da suka halarci taron nadin sarautar, Oba Oyekon Adekomi, Shugaban majalisar karamar Hukumar Badagry ya shaida wa Aminiya kyakkyawar alakar jama’ar Arewa da sauran kabilun yankin. Ya ce su tsintsiya madaurinki daya ne, kuma suna aiki tukuru a tare, domin ganin yankin ya ci gaba.
Alhaji Abdullahi Musa danmalle, wanda jami’in rundunar ‘yan sanda ne, kuma masarautar ta nada shi Barden yaki, ya shaida wa Aminiya cewa, abin da ya ba shi sha’awa ya karbi sarautar gargajiya, shi ne, bauta wa jama’a tare da kare hakkokinsu. Shi kuwa Alhaji Sulaiman Umar Gogori, wanda aka nada Sarkin Samarin Hausawan Samiboda, cewa, ya yi kasancewar matasa su ne kashin bayan al’umma zai yi tsayin daka don ganin rayuwarsu ta inganta, tare da ba su kulawa ta musanman.
Kakakin majalisar masarautar samiboda, Usman Umaru cewa, ya yi karin sababbin nade-naden zai kara wa masarautar daukaka, kana ya yi kira ga sababbin ‘yan majalisar da hakiman su himmatu don ci gaba da samun hadin kai a masarautar.
Maimartaba Sarkin Hausawan Legas, kuma shugaban majalisar masarautar jihar Alhaji Sani Kabir kira ya yi ga wadanda aka yi wa nadin da su riki amana; kuma su yi adalci domin sai da adalcin shugabani ne talakawansu za su bisu. Ya yaba da yadda jama’a suka yi dafifin halartar taron wanda ya ce hakan na nuni da hadin kan al’umar yankin.
Taron ya samu halartar manyan sarakunan ciki da wajen Legas, wadanda suka hada da Sarkin Kwatakwalawa da Fulani da kuma mashahuran mawakan gargajiya da suka nisahadantar da al’umma.