Sarkin Jama’a ya kira taron sarakuna kan zaman lafiya

A yunkurinsa na ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a Kudancin Kaduna, Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya kira taron sarakunan karamar Hukumar Jama’a, inda suka tattauna kan tashe-tashen hankulan da suke faruwa a tsakanin manoma da makiyaya a yankin.Taron wanda ya gudana a fadar Sarkin Jama’a da ke garin […]

Sarkin Jama’a ya kira taron sarakuna kan zaman lafiya
Sarkin Jama’a ya kira taron sarakuna kan zaman lafiya

A yunkurinsa na ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a Kudancin Kaduna, Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya kira taron sarakunan karamar Hukumar Jama’a, inda suka tattauna kan tashe-tashen hankulan da suke faruwa a tsakanin manoma da makiyaya a yankin.
Taron wanda ya gudana a fadar Sarkin Jama’a da ke garin Kafanchan ya jawo hankalin sarakuna, a matsayinsu na iyayen kasa da kada su yi kasa a gwiwa a duk lokacin da wani rikici ya sake kunno kai don magance  sake faruwarsa.
 Bayan sauraron bayani daga wakilin masarautar Godogodo kan abin da ya faru a yankinsu, Sarkin  Jama’a da sauran mahalarta taron sun nuna rashin jin dadinsu kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka tafka a kauyukan Ninte da Gada-Biyu, inda Sarkin ya nanata bukatar samun hadin kai a tsakanin sarakunan yankin.
A karshe an zartar da shawarar kafa wani kwamiti da zai zauna da makiyaya da manoma a lokuta daban-daban domin jin korafin kowannensu domin gano bakin zaren, kuma za a rika ci gaba da zama irin wannan don samun fahimtar juna.
Dukkan mahalarta taron sun yaba wa Sarkin kan wannan matakin da ya dauka. Kuma daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Shugaban karamar Hukumar Jama’a, wanda Mataimakinsa John Gambo Kanufi ya wakilta, sai Sarkin Kagoma da Sarkin Kaninkon yayin da sarakunan Godogodo da Fantsuam da na Barde suka turo wakilansu.