Sarkin Jere Sa’ad Usman ya rasu

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Jere da ke Jihar Kaduna, Dokta Sa’ad Usman, rasuwa bayan ya sha fama da rashin lafiya sakamakon raunin da ya yi yayin wani rikici a yankin. Kanin marigayin, Aminu Jere, shi ya sanar da rasuwar Sarkin. “Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun. Yanzun nan na yi rashin dan […]

Sarkin Jere Sa’ad Usman ya rasu

Marigayi Sarkin Jere Sa’ad Usman ya rike mukaman gwamnati da dama

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Jere da ke Jihar Kaduna, Dokta Sa’ad Usman, rasuwa bayan ya sha fama da rashin lafiya sakamakon raunin da ya yi yayin wani rikici a yankin.

Kanin marigayin, Aminu Jere, shi ya sanar da rasuwar Sarkin.

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun. Yanzun nan na yi rashin dan uwana Sarkin Jere, Dokta Sa’ad Usman”, inji Aminu, wanda ya kara da cewa, “Za a yi sallar janazah a garin Jere da karfe 2.00 na rana”.

Marigayin dai miji ne ga tsohuwar Ministar Kudi a zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, kuma tsohuwar ’yar Majalisar Dattawa, Esther Nenadi Usman.

Ya kuma taba rike manyan mukamai a gwamnatin Jihar Kaduna, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jiha.

 

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro

’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato