Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya
Ta rasu ne a safiyar Lahadi kamar yadda sarkin malamai na masarautar malam Jibrin Yakubu Adam ya tabbatarwa Aminiya.
Mai martaba sarkin Jiwa a yankin birnin tarayya Abuja, Alhaji Idris Musa ya yi rashin mahaifiyarsa mai suna Hajiya Ramatu Ibrahim.
Ta rasu ne a safiyar Lahadi kamar yadda sarkin malamai na masarautar malam Jibrin Yakubu Adam ya tabbatarwa Aminiya.
Hajiya Mai Babbar Ɗaki, kamar yadda ake yi mata laƙabi, ta rasu ta bar ‘ya’ya huɗu da kuma jikoko sama da 30. Ya ce, an gudanar da janaiza tare da binneta a Babbar maƙabartar Garin Jiwa a ranar ta Lahadin.
Cikin waɗanda suka halarci jana’izar akwai Sarkin Bwari Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro, da Gomo na Kuje Alhaji Haruna Tanko Ibrahim, da Sarkin Pai Alhaji Abubakar Sani Pai, sai kuma shugabannin ƙananan hukumomin Birnin Abuja da kewaye (AMAC) da kuma takwaransa na Abaji, wato Mista Christopher Zakka Mai Kalangu da malam Abubakar Umar Abdullahi.
A yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai ga sarkin Jiwa a ranar Litinin, Sarkin Rubochi da ke yankin Kuje a Abuja, Alhaji Muhammad Ibrahim Pada, ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa ta gari da ta samar da kyawawan tarbiyya abin koyi ga ‘ya’yanta, inda ya yi addu’ar Allah Ya gafarta mata da kuma yi mata rahama da Aljannah.