Sarkin Kaltungo ya koya jama’arsa dabarun noman rogo na zamani

Basaraken ya nuna sabbin dabarun shuka ga al’umma, inda ya nuna sauki da ingancinsu wajen kara yawan amfanin gona da inganta girbi

Sarkin Kaltungo ya koya jama’arsa dabarun noman rogo na zamani

Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad, ya kaddamar da dabarun noman rogo na zamani a masarautarsa tare da kira ga al’ummarsa su rungumi harkar.

Basaraken ya yi hakan ne a  kokarinsa na yaki da yunwa da bunkasa harkar noma a tsakanin talakawansa, a yankin Ture Balam da ke Karamar Hukumar Kaltungo a Jihar Gombe.

Mai Kaltungo ya jaddada muhimmiyar rawar da noman rogo ke takawa wajen tunkarar kalubalen samar da abinci, inda ya bayyana cewa hakan na iya bunkasa abinci ba tare da tsadar taki ba.

Da yake kaddamar da noman rogon na zamani, basaraken ya nuna sabbin dabarun shuka ga al’umma, inda ya nuna sauki da ingancinsu wajen kara yawan amfanin gona da inganta girbi.

Sarkin ya ja hankalin al’umma da su rungumi noman rogo, inda ya bayyana alfanun da suke samu a fannin tattalin arziki da juriya kan tsadar taki.

Sai ya yi nuni da cewa tsadar takin zamani ta sa noman rogo ya zama zabi mai dorewa kuma mai sauki ga manoma.

Hakazalika ya nuna ingantattun hanyoyin samar da noman kasa da hanyoyin amfani da ruwa, tare da kawar da takin mai magani.

Ya kuma rarraba kayayyaki don taimaka wa manoma wajen aiwatar da wadannan ayyuka.

Manoman yankin da suka hada da Buba Dala da Abdullahi Baba, sun yaba da shirin, inda suka bayyana fatansu na inganta ayyukansu da kuma kara samar da ayyukan yi.

Rashida Lewi ta yaba wa tsarin sarkin wanda ke bai wa manoma ilimin da suke bukata don samun nasarar noman rogo.

Rabaran Tukur Fika mai ritaya, ya yaba da shirin, inda ya bayyana hakan a matsayin nuna kyakkyawan jagoranci da jajircewa wajen kyautata rayuwar al’umma.