Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Marubuta da kishin kasa

Ga duk mai kula da al’amuran yau da kullum, ya dade da sanin wane ne Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, don haka ba lallai ne a yi masa wata gabatarwa ba. Amma domin saita maudu’inmu na yau, ya zama dole mu zayyana wani bangare na gabatarwar, musamman ta abin da ya danganci maudu’in.Ida nana maganar […]

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Marubuta da kishin kasa
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Marubuta da kishin kasa

Ga duk mai kula da al’amuran yau da kullum, ya dade da sanin wane ne Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, don haka ba lallai ne a yi masa wata gabatarwa ba. Amma domin saita maudu’inmu na yau, ya zama dole mu zayyana wani bangare na gabatarwar, musamman ta abin da ya danganci maudu’in.
Ida nana maganar kishin kasa, fadakarwa, tsokaci da sharhi ta bangaren addini, al’ada, al’amuran yau da kullum, marubuci na daga cikin wadanda ke aikin gina kasa da al’umma. Don haka, Sarkin Kano, tun kafin ma ya zama sarki, ya kasance marubuci, malami kuma shugaba. Dalili ke nan ma ga duk wanda ya san shi, ya san ya yi tsokace-tsokace, sharhe-sharhe da tunasarwa ta hanyar kafafen watsa labarai, musamman ma jaridar Weekly Trust da Daily Trust na shekarun baya. Haka kuma, a duk inda aka gayyace shi domin gabatar da lacca ko wani jawabi, yakan fito fili ya bayyana sakonsa na gyara game da al’amuran da suka shafi al’amuran kasa.
A lokacin da ya zama Sarkin Kano kuwa, mutane da dama sun zaci zai canza daga alkiblarsa, zai rika yin gum da bakinsa, kamar yadda aka san sarakunan gargajiya suna yi a wannan bangare na Arewa. Sai dai abin da mutane ba su sani ba shi ne, Hausawa suna cewa, hali zanen dutse ne, don haka babu dalilin da zai sanya sarkin ya zama baya, musamman wajen tsokaci, fadakarwa da nusarwa ga al’umma. Haka kuma, mutane sun mance ko kuma sun sha’afa, cewa shugaba na kwarai, dole ne ya kasance jagora ta fuskar nasiha, jagora da ankararwa. Don haka har yanzu dai sarkin yana nan kan hanyarsa – shugaba, jagora, marubuci kuma malami.
A matsayinsa na ‘Shugaba’ kuma sarki mai wukar yanka mai daraja ta daya, Malam Muhammadu Sanusi II bai bar aikinsa na fadakarwa, tsokaci, tunasarwa ga al’umma ba, dalilin da ya sanya har wasu ma da ba su ankara da muhimmancin aikin nasa ba suke ganin bekensa, har suna cewa ya kamata ya daina wadannan muhimman ayyuka. Dalili ke nan ma ya sanya wadanda suka san shi, suka san halayensa kuma suka san muhimmancin aikin da yake yi, suka nemi al’umma su fahimce shi, su kara masa kwarin gwiwa kuma su ba shi goyon baya, domin ci gaba da wadannan muhimman ayyuka na kishin kasa.
daya daga cikin mashahuran marubutan wannan zamani, Magaji Galadima, Galadinan Maitsidau, yana daya daga cikin mashahuran mutanen da suka san Sarkin Kano, sani na hakika. Yana daya daga cikin wadanda suka sani kuma suka gane muhimmancin duk wadannan ayyuka da sarkin yake yi. Dalili ke nan ya yi ta neman hanyoyin da zai bi domin ya ankarar da al’umma, musamman ma abokansa marubuta, domin su ma su gane wadannan manyan kudurori na kishin kasa da Sarki Muhammadu Sanusi II yake aiwatarwa.
A matsayinsa na marubuci, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kuma aboki ga sauran marubuta na zamaninsa, Malam Magaji Galadima, sai ya ga cewa ga dama ta samu, inda za a hadu a jaddada zumuncin juna, a fadakar da juna sannan a kara wa juna kaimi, domin a ci gaba da aikin kishin kasa na tsokaci, sharhi da fadakarwa. Dalili ke nan a Juma’ar da ta gabata, 1 ga Janairu, 2016, ta kasance ranar farin ciki ga shi Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, musamman saboda ranar ce ta kasance ya aurar da diyarsa ta farko a rayuwarsa. Zaratan marubuta da ’yan jarida sun halarci wannan daurin aure domin taya sarkin murna tare da sada zumunci da juna.
Bayan an daura auren Saudat Shahida Sanusi da angonta Abdulkadir Baba Ahmad da misalin karfe 10 na safe, sai kuma marubuta da ’yan jarida, karkashin jagorancin Galadiman Maitsidau, Malam Magaji Galadima suka kebe a natsattsen wuri, suka gana da juna, suka fadakar da juna kuma suka sada zumunci da juna, kamar kuma yadda suka gaya wa juna gaskiya na abubuwan da suka kamata su rika yi da nufin kishin kasarsu da al’ummarsu.
Wasu daga cikin hanshakan marubuta da ’yan jaridar, sun hada da Malam Ibrahim Sheme da Dokta Sherrif Almuhajir da Ashafa Murnai Barkiya da Malam Yasir Ramadan Gwale da Malam Yakubu Musa da Malam Jaafar Jaafar da Malam Anas Saminu Ja’en. Sauran sun hada da Abdul’azeez Abdul’azeez da Suleman Ya’u  da Al-Amin Chiroma da Dokta Abdullahi dahiru da ni kaina Bashir Yahuza Malumfashi da kuma jajirtattar marubuciya, ’yar jarida, Hajiya Sa’adatu Baba Ahmad.
A yayin da yake tsokacinsa, Magaji Galadima ya nusar da marubuta da mu gane tasirin abin da muke rubutawa ga al’umma. Ya ja hankalinmu da cewa lallai rubutu abu ne mai matukar tasiri, domin kamar yadda aka sani, alkalami ya fi takobi. Ya neme mu da cewa duk abin da za mu rubuta, mu tabbatar mun auna shi, mun jinjina shi ta yadda zai zama mai amfani ga kawunanmu, ga al’ummarmu da kuma kasarmu gaba daya. Ya ce duk abin da za mu yi, mu tabbatar mun kare martabar shugabanninmu da addininmu da kyawawan al’adunmu. Ta haka ne kuma ya nemi mu rika nuna kishin kasa da kishin mutanenmu a duk inda muke.
Marubucin nan kuma dan jarida mai tashe, Malam Jaafar Jaafar, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa, inda ya nemi marubuta da su rika daraja juna, su ruka mutunta ra’ayin juna. Ya yi kira ga musamman masu tsokaci ta hanyar kafafen sadarwa na intanet da mu rika kauce wa yakar juna da munanan kalamai. Kamar yadda ya ce, kowa na da ’yancin fadin albarkacin bakinsa, amma kada a rika daukar al’amuran da zafi, mu kauce wa cin zarafin juna.
Haka shi ma Dokta Sherrif Almuhajir, a yayin da yake nasa tsokacin, ya ji dadin yadda a karon farko ya fara haduwa da wasu marubutan da ya dade yana ji kuma yana karanta ayyukansu. Bisa harkar rubuce-rubuce kuwa, malamin ya nemi marubuta da su rika tantance abin da suke rubutawa kafin su watsa su ga al’umma. Musamman ya nemi cewa lallai ne duk abin da mutum zai rubuta, ya yi bincike tukunna, domin bayyana hakikanin abin da yake na gaskiya, wanda kuma zai fadakar kuma ya zama mai amfani ga al’umma.
Kamar sauran masu tsokaci, marubuci kuma dan jarida, Malam Abdu’azeez Abdul’azeez shi ma goyawa ya yi a kan sauran kininsa, inda ya kara nuna muhimmancin sanya kishin kasa da kishin al’umma a yayin rubutu. Ya buga misali da su Malam Magaji Galadima, wadanda ya ce sun yi ta aikin tsokaci da rubuce-rubuce tun farkon shigowar fasahar zamani.
Malam Al-Amin Chiroma ma ya tofa nasa miyan, inda ya nemi lallai marubuta su kasance tsintsiya daya, masu tunkarar al’amari daya na fadakarwa, kishin kasa da kishin al’umma.
Daga karshe dai an gaisa da juna, an yi zumunci kuma an dauki hotunan tarihi sannan Malam Yasir Ramadan Gwale ya rufe mana da addu’a.
Babu shakka wannan taro ya kara tabbatar mani da cewa lallai Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ingantaccen shugaba ne, hamshakin sarki ne, malami ne kuma marubuci ne da kowa ke darajawa. Allah Ya kara wa shugabanninmu daraja da fikira, Ya kara musu imani da karfin niyyar adalci ga al’umma, amin.