Sarkin Kano: Yadda Sanusi II na shirye-shiryen komawa kujerarsa
Sanusi ya fara shirye-shiryen dawowa kan kujerar Sarkin Kano cikin kasaita
Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sanusi II na daf da komawa kan kujerarsa.
Majiyoyin sun ce a Alhamis din nan Gwamna Abba Kabir Yusuf zai rattaba hannu kan dokar masarautu da majalisar dokokin jihar ta yi wa kwaskwarima.
Wata majiya ta shaida mana cewa, “yanzu haka Sarki Sanusi II na shirye -shiryen komawa kan kujerarsa; Duk da cewa yanzu ba ya gari ya yi bulaguro, amma muna sa ran zuwa gobe Juma’a zai komo Kano.”
Wata majiyar kuma ta tsegunta mana cewa Sanusi yana Jihar Legas inda yake shirye-shiryen dawowa cikin kasaita.
Aminiya ta ruwaito cewa gyaran dokar ne ya kai ga soke duk masarautu biyar da ke jihar, wadanda aka samar a ranar 5 ga Disamba, 2019, a zamanin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A wancan lokacin ne gwamnatin rabe Masarautar Kano zuwa gida biyar da suka hada da masautun Kano, Bichi Gaya, Karaye, da kuma Rano.
Bayan saukar Ganduje da hawan gwamantin NNPP mai rinjaye a majalisar, a ranar 23 aka soke dokar ‘Masarautun Ganduje’ da duk mukamai da sauye-sauyen da ta samar.
Aminu da Nasiru Ado Bayero ba sa Kano
Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da Sarki Kano da ya maye gurbin Sanusi II, Aminu Ado Bayero da dan uwansa wanda shi ma aka sauke, Nasiru Ado Bayero suka yi bulaguro.
Ana iya tuna cewa Muhammadu Sanusi II a zama Sarkin Kano na 14 ne bayan rasuwar Sarki Ado Bayero, mahaifin Aminu da Nasiru.
A ranar Laraba, da aka fara karatun soke dokar ‘Masarautun Ganduje’ Sarki Aminu Ado Bayero, ya kai ziyara ne Sarkin Kasar Ijebu, Oba Sikiru Adetona, Awujale, domin taya shi murnar cike shekaru 90 a duniya, da kuma shekaru 64 a kan karaga.
A daya bangaren kuma, kaninsa, Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero, muna samu labarin cewa yana kasar waje, ko da yake kawo yanzu ba mu iya tantance hakan ba.
Haka zalika ba mu samu bayani game da inda sarakunan Gaya, Karaye da Rano, suke ba har zuwa lokacin da muka kammala wannan labarin.
Kano Babu Sarki —Majalisar Kano
Aminiya ta ruwaito cewa bayan kammala zaman majalisar na ranar Alhamis, Shugaban Masu Rinjaye, Lawal Hussaini Chediyar Yan Gurasa, ya bayyana cewa a halin da ake ciki babu sarki a Jihar Kano sai idan Gwamna ya nada sabo.
Chediyar Yan Gurasa ya ce, “yanzu, babu sarki a Jihar Kano har sai gwamna ya amince da naɗa wani sabon.”
“Yanzu [Jihar] Kano za ta zama da sarki guda daya, idan gwamna ya sa hannun a kan dokar, an rushe wadannan masarsutun babu su,” in ji Chediyar ’Yan Gurasa.
Rawar da Kwankwaso ya taka
Za a tuna cewa wata guda kafin hawan Gwamna Abba bisa kujera, tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran NNPP a Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda gwamnatinsa ta fara nada Sanusi II, ya ce sabuwar gwamnatin NNPP za ta soke sabbin masarautun.