Sarkin Kano ya bukaci habaka kasuwancin Gambiya da Najeriya
Shugaban Gambiya ya ba da tabbacin habaka kasuwanci tsakanin kasarsa da Najeriya
Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga duk wani shiri da zai hada kan ‘yan kasuwar Gambiya da na Najeriya, musamman Jihar Kano.
Da yake magana a lokacin da ya ziyarci Shugaban Kasar Gambiya, Mista Adama Barrow, ranar Litinin, Sarkin ya ce lokacin kulla alaka ya zo “domin muna da jiragen sama masu zirga-zirga kai-tsaye a tsakanin kasashenmu biyu.”
- TNM za ta samar wa ‘yan Najeriya mafita a 2023 —Kawu Sumaila
- DAGA LARABA: Yadda labaran karya ke buya a tsakanin al’umma
Sarkin ya sanar da Mista Barrow cewa Kano, a matsayinta na jiha mafi yawan al’umma a Najeriya, babbar cibiyar kasuwanci ce tun shekaru aru-aru.
Ya ce hakan ne ya sa ya debi mambobin Kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai ta Kano da nufin ganawa da takwarorinsu na kasar Gambiya domin lalubo hanyoyin hadin gwiwa.
Da ya ke jawabi, Shugaba Barrow ya gode wa Sarkin bisa ziyarar da ya kai masa, ya kuma ba shi tabbacin cewa zai duba hanyoyin da za a bi don inganta alaka tsakanin ‘yan kasuwar Gambiya da na Najeriya, musamman na Kano, duba da dimbin kamanceceniya da ke tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Ya kuma yi nuni da cewa, ziyarar za ta taimaka matuka wajen samar da alakar da za ta inganta ‘yan uwantaka a yankin Afirka ta Yamma baki daya.