Sarkin Kano ya bukaci malamai su rika wa’azin karfafa hadin kai
Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II, ya bukaci al’ummar Musulmin kasar nan, musamman malaman addini su karfafa hadin kan al’umma, maimakon yin abubuwan da za su kawo rarrabuwa a tsakaninsu.Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, a karkashin jagorancin […]
Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II, ya bukaci al’ummar Musulmin kasar nan, musamman malaman addini su karfafa hadin kan al’umma, maimakon yin abubuwan da za su kawo rarrabuwa a tsakaninsu.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, a karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa a ranar Litinin.
Sarkin ya ce a duk lokacin da aka samu al’ummar Musulmi kansu a rabe suna fada, to ba wanda yake cin riba, sai wanda ba Musulmi ba, “Kullum abin da muke nuna wa malamai shi ne akwai sabani wanda ya dade a tsakanin al’umma, kuma ba za a daina yin sa ba, sannan akwai abubuwan da suka hada mu da suka fi wadanda muke sabani. Musulunci na fuskantar kalubale, masu fada da shi ba ruwansu da wata kungiya, Musuluncin suke fada da shi. Don haka akwai bukatar hada kan Musulmi don tunkarar wannan kalubale”.
Ya ce wajibi ne malamai su fi kowa aiki da usulubi na hikima wajen wa’azi da kiran mutane zuwa ga addini ko fahimtarsu, kamar yadda Allah Ya umarci Annabi Musa da Haruna lokacinn aikensu zuwa ga Fir’auna da kuma yadda Ya ce, kada a yi jayayya da Ma’abuta Littafi face da magana wadda take mafi kyau.
Sarki Sanusi ya ce ya kamata a duba mene ne ya fi muhimmanci ko da abu na bukatar gyara, in aka ga maida hankali kan gyara zai kawo barnar da ta fi shi, to a hakura sai wani lokaci.
Daga nan sai ya bayyana cewa gidan sarautar Kano gida ne na daukacin kungiyoyin Musulunci, “Mu abin da gidan nan ya gada, duk kungiyoyi na Musulunci da na da’awa nan gidansu ne, kuma ba ma shigar da kanmu cikin rarrabuwa, domin rarrabuwar malamai tana kaiwa ga rabuwar al’umma, rabuwar al’umma na jawo koma baya da rauni,” inji shi.
Tunda farko shugaban kungiyar, Sheikh Bala Lau ya ce sun je fadar ne domin mubaya’a da taya sabon Sarkin murna tare da yi masa ta’aziyyar rasuwar marigayi Sarkin Kano, inda ya bayyana sabon sarkin da dalibin ilimi mai taimakon addini.
Shehin Malamin ya ce, “Muna fata Allah Ya yi amfani da Sarkin wajen hada kan al’ummar Musulmin jihar da na kasar nan baki daya”. Ya tunatar da Sarki Sanusi cewa Musulunci ne ya kafa gidajensu, don haka sun gaji aikin yada Musulunci da da’awa da inganta rayuwar Musulmi, don haka ya dora kan haka daga inda magabatansa suka tsaya.
Daga cikin wadanda suka rufa wa shugaban baya har da Sakataren kungiyar na kasa, Sheikh Muhammad Kabiru Gombe da shugaban kungiyar a Jihar Kano, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan da Sheikh Alhassan Sa’id Jos da Sheikh Yakubu Musa Katsina da Sheikh Habibu Yahaya kaura da Sheikh Abubakar Giro Argungu da sauransu.