Sarkin Kano ya je ta’aziyyar Sarauniyar Ingila
Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya je ziyarar ta’aziyyar rasuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II a ofishin jakadancin Birtaniya da ke Abuja. Sarkin ya je ziyarar ta’ziyyar ce a ranar Litinin a ofishin, inda ya sami tarbar Jakadar Birtaniya a Najeria, Catriona Laing. Yadda rasuwar Sarauniyar Ingila ta kawo wa ’yan kasuwa ciniki […]
Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya je ziyarar ta’aziyyar rasuwar Sarauniyar Ingila, Elizabeth II a ofishin jakadancin Birtaniya da ke Abuja.
Sarkin ya je ziyarar ta’ziyyar ce a ranar Litinin a ofishin, inda ya sami tarbar Jakadar Birtaniya a Najeria, Catriona Laing.
- Yadda rasuwar Sarauniyar Ingila ta kawo wa ’yan kasuwa ciniki
- HOTUNA: Ziyarar Sarkin Kano Da Na Bichi Ga Sarkin Musulmi
Sarkin na Kano ya hannu a wani littafin ta’aziyyyar ne da aka tanada a bisa al’ada a yammacin ranar.
Ya kuma nuna alhininsa dangane da rashin, ya kuma janta wa al’ummar Ingila da kuma duniya baki daya a bisa wannnan babban rashi.
A yayin ziyarar dai, Sarkin na Kano ya sami rakiyar wasu daga cikin manyan hadimai da ’yan majalisar masarautarsa.