Sarkin Kano ya nada manyan hakimai guda biyu

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na II ya nada manyan hakimai biyu a masarautar Kano a ci gaba da shirinsa na kara kafa mulkinsa tun lokacin da ya hau karagar mulki a watan Yunin da ya gabata.Manyan hakiman da ya nada sun hada da Alhaji Mannir Sunusi a matsayin danmajen Kano, wanda kuma […]

Sarkin Kano ya nada manyan hakimai guda biyu
Sarkin Kano ya nada manyan hakimai guda biyu

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sunusi na II ya nada manyan hakimai biyu a masarautar Kano a ci gaba da shirinsa na kara kafa mulkinsa tun lokacin da ya hau karagar mulki a watan Yunin da ya gabata.
Manyan hakiman da ya nada sun hada da Alhaji Mannir Sunusi a matsayin danmajen Kano, wanda kuma dan marigayi Sarki Muhammadu Sunusi ne. Hakimi na biyu da aka nada shi ne Alhaji Yahaya Inuwa Abbas a matsayin Dokajin Kano.
Alhaji Mannir Sunusi ya maye gurbin sabon Sarkin ne a wanda kafin nada shi Sarki, shi ne danmajen Kano.
Sabon Dokajin Kano ya fito ne daga gidan marigayi Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Inuwa, inda jama’a ke ganin wani mataki ne na jawo gidajen sarautar Kano a jiki tare da hada kan ’ya’yan masarautar da Sarki Sanusi na II ke yi.
A jawabin Sarki Sanusi na II bayan nadin, ya yi kira ga sababbin hakiman su jajirce tare da ba da goyon baya wajen ciyar da masarautar gaba da kuma kare martabarta. Kuma ya bukaci hadin kansu a matsayinsu ’yan uwansa don taimaka masa wajen gudanar da mulki a cikin nasara.
A jawabin sabon Dokajin Kano, Alhaji Yahaya Inuwa Abbas ya sha alwashin yin bakin kokarinsa wajen bayar da gudummawarsa don ganin masarautar ta kara samun daukaka tare da cimma nasara.
Wannan shi ne karo na biyu na bikin nadin sarauta da Sarkin Muhammadu Sunusi na II  ya yi tun hawansa karaga, inda a farkon hawansa ya nada sabon Wazirin Kano, Alhaji Sa’adu Gidado.