Sarkin Kano Ya Nada Sabon Walin Kano, da Sarkin Bai
Mai dakin sabon Sarkin Bai, Hadiza Mansur, ta yi addu’ar Allah
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada Bashir Mahe Bashir Wali a matsayin Walin Kano, da kuma Masur Mukhtar a matsayin Sarkin Bai.
Bashir Mahe dai yanzu shi ne Walin Kano na Bakwai, bayan ya gaji mahaifnsa da yayi murabus saboda yawan shekaru da kuma rashin lafiya.
- Asibitin Kano mai shekara 106 da ke da likita 1 kacal
- Elon Musk Ya Saye Twitter ya kori jagororin kamfanin
Shi ma da Mansur Muktar da tsohon ministan kudi ne, kuma mataimakin Shugaban Bankin raya mususlinci, ya zamo Sarkin Ban Kano na Tara.
Kafin rasuwar mahifinsa, shi ne mafi dadewa a tarihin Majalisar Masarautar Kano, tun kafa ta a karni na 19.
Ya shafe shekaru 63 a matsayin Hakimi, kuma Dan Majalisar Sarki, kana guda daga masu nada Sarkin Kano, har zuwa rasuwarsa, a lokacin yana da shekaru 95 a duniya.
Da take ganawa da Aminiya, mai dakin sabon Sarkin Bai, Hadiza Mansur, ta yi addu’ar Allah Ya yi masa jagora.
A hannu guda bikin nadin ya samu halartar manyan ’yan siyasa, da Sarakuna da dama daga ciki da wajen Kano.