Sarkin Kano ya samu gagarumar tarba

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya samu gagagrumar tarba daga dubban jama’a a filin jirgin saman Malam Aminu Kano lokacin da ya dawo daga jinya daga birnin Dubai na Hadaddiyyar Daular Larabawa a shekaranjiya Laraba.Dubban mutane kuma sun yi jerin gwano a gefen titi suna yi wa Sarkin maraba da dawowa bayan ya […]

Sarkin Kano ya samu gagarumar tarba

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero yana sauka daga jirgin sama a shekaranjiya Laraba, a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano a bayansa Aminu Ado Bayero ne. Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya samu gagagrumar tarba daga dubban jama’a a filin jirgin saman Malam Aminu Kano lokacin da ya dawo daga jinya daga birnin Dubai na Hadaddiyyar Daular Larabawa a shekaranjiya Laraba.
Dubban mutane kuma sun yi jerin gwano a gefen titi suna yi wa Sarkin maraba da dawowa bayan ya shafe kusan wata uku a waje. Idan za a iya tunawa a ranar 12 ga watan Yulin da ya gabata ne Sarkin ya bar kasar nan don zuwa jinya jim kadan da kammala bikin cikarsa shekara 50 a gadon sarauta.
Wani jirgin saman mayakan sama na Najeriya mai lamba 5N-FGb ne ya kawo Sarkin da tawagarsa, inda ya sauka da misalin karfe 4:25 na yammacin ranar Larabar.
Daga nan sai Sarkin ya shiga motarsa kirar Rolls Royce zuwa fadarsa, tare da rakiyar dimbin jama’a ciki har da Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Farouk Umar Farouk da Sarkin Ringim Alhaji Sayyadi Mahmoud Ringim da Wamban Kano Alhaji Abbas Sunusi da Walin Kano Alhaji Mahe Bashir Wali da Sa’in Kano Alhaji Wada Waziri da Makaman Kano da Hakimin Kura da na Dala, Alhaji Aminu Ado Bayero da Hakimin Taruni, Alhaji Nasiru Ado Bayero da fitattun ’yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati.
A hirarsa da ’yan jarida, wakilin Gwamnan Jihar Kano a wurin tarbar kuma Kwamishinan Ayyuka na Nusamman, Janar Idris Bello Dambazau ya ce “A madadin gwamnatin Jihar Kano, muna bayyana farin cikinmu da dawowar Mai martaba Sarki, wanda kowa ya san ya yi tafiyar ne saboda rashin lafiya, ga shi Ubangiji Ya dawo mana da shi lafiya, muna murna kwarai da gaske.”
Wakilin Ooni na Ife kuma Sakatarensa, Alhaji Moshood Abimbola ya ce an umarce shi ne ya zo Kano, musamman don ya yi wa Sarkin barka da zuwa, sakamakon sakon da Sarkin ya aike wa Ooni cewa zai dawo Najeriya a wannan rana.
daya daga cikin ’ya’yan Sarkin kuma Hakimin Dala, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana farin ciki tare da godiyarsa ga Ubangiji da Ya ba Sarki lafiya. Haka ya yi godiya ga daukacin jama’ar Kano bisa addu’o’in da suka yi ga Sarkin a yayin rashin lafiyarsa.