Sarkin Katsina ya ce babu sauran cutar poliyo a Jihar Katsina

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya ce a yanzu babu sauran cutar poliyo a Jihar Katsina. Sarkin ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a filin kofar Soro a ranar bikin karamar Sallah a makon jiya.Sarkin wanda ya bayyana irin hadin kan da masarautarsa ta bayar tun daga kan hakimai […]

Sarkin Katsina ya ce babu sauran cutar poliyo a Jihar Katsina

Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir UsmanMai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya ce a yanzu babu sauran cutar poliyo a Jihar Katsina. Sarkin ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a filin kofar Soro a ranar bikin karamar Sallah a makon jiya.
Sarkin wanda ya bayyana irin hadin kan da masarautarsa ta bayar tun daga kan hakimai zuwa ga masu unguwanni da talakawa ga shirin allurar rigakafin cutar poliyo ya ce,”sakamakon ba mu hadin kai da aka yi kan yaki da cutar poliyo, yau ina kyautata zaton babu poliyo a Jihar Katsina. Wannan godiya ce zan kara yi muku. Mun yi farin ciki kwarai da aka amshi wannan abu, kuma insha Allahu mun ga bayanta ke nan.”
Dokta Abdulmumini ya yi kira a kara mayar da hankali a wajen dashen itatuwa, musamman a yanzu da ake cikin damina, domin yaki da kwararowar hamada. Sai ya shaida wa hakimai da dagatai da masu unguwanni da manoma da sauran al’umma bullo da wata gasa don karrama duk wanda ya yi zarra a dashen itatuwa.
Sarkin na Katsina ya yi kira a kan batun zaman lafiya, inda ya ce yadda ake ta samun tashe-tashen hankulla da asarar rayuka abin takaici ne. “A kan haka nake kira ga hukumomi su kara kula tare da yin duk abin da ya kamata don tallafa wa masu unguwanni wadanda su ne jami’an tsaro na farko a cikin al’umma, amma har yanzu alawus din da ake ba su bai taka kara ya karya ba. Idan aka tura dan sanda ko soja ko wani jami’in tsaro zuwa unguwa ba zai iya nuna wannan gidan Rabo ko Hashimu ba ne, amma mai unguwa ko yana barci ka ce ya kai ka gidan Idi babu shakka zai kai ka. Shi ne wanda yake kula da shigi da ficin jama’ar unguwarsa. Don haka nake rokon gwamnatocin kasar nan, su yanka wa masu unguwanni albashi ba wai karin alawus kawai ba.”
Sarkin ya yi kira ga matasa su guji zaman banza, su rika yin sana’a komai kankantarta don ta fi yawon maula ko bangar siyasa.