Sarkin Katsina ya dora laifin jefa Arewa a halin da ake ciki a kan ’ya’yanta
Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya aza alhakin halin da Najeriya, musamman yankin Arewa ke ciki na bala’o’in da yake fuskanta a kan ’yan Arewa.Sarkin ya ce, ’yan Arewa suna sane da irin halin da yankin ya shiga na matsaloli, amma kadan ne daga cikinsu ke tambayar me ya sa wadannan masifu […]

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya aza alhakin halin da Najeriya, musamman yankin Arewa ke ciki na bala’o’in da yake fuskanta a kan ’yan Arewa.
Sarkin ya ce, ’yan Arewa suna sane da irin halin da yankin ya shiga na matsaloli, amma kadan ne daga cikinsu ke tambayar me ya sa wadannan masifu sai a Arewa kadai ake fuskantarsu?
Sarkin, wanda ya bayyana haka a ranar Asabar da ta gabata lokacin da yake jawabi a wajen nadin sarautu ga wasu daga cikin ’ya’yan masarautarsa, ya ce, “Rashin tsarkake zukatanmu ne ya jefa mu cikin wadannan wahalhalu.”
Dokta Abdulmuminu Kabir ya ce, domin samun zaman lafiya da ci gaban yankin Arewa ya zama dole mu ajiye duk wani matsayin da muke da shi don mu hada kai waje daya ta hanyar nuna wa juna soyayya da taimakon junanmu, ya ce ta wannan hanyar ce kadai za mu ceto tare da farfado da yankin Arewa daga cikin irin mawuyacin halin da yake ciki. “Ya zama wajibi ga shugabanni su rungumi jama’arsu, su rika taimakonsu kuma su
rika aiki tare da wadannan al’umma tasu,” injii Sarkin Katsina.
Ya nanata kudurin masarautarsa na kare hakki da muradun talakawansa inda ya ce, su ne gaba da komai a wajensa domin in babu su ba abin da zai jagoranta.
Da ya juya a kan wadanda aka nada, Sarkin ya gargade su da su ji tsoron Allah kuma su sani cewa wani karin nauyi ne ya hau kansu, don haka su gudanar da jagorancinsu cikin adalci.
Wadanda Sarkin na Katsina ya nada a fadarsa da ke kofar Soro, cikin birnin Katsina, sun hada da Mukaddashin Shugaban Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Tarayya (FIRS), Alhaji Kabir Muhammad Mashi a matsayin Kaigaman Katsina, sai Kwamishinan Gona na Jihar Katsina, Alhaji Musa Adamu Funtuwa a matsayin dankafin Katsina da Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri a matsayin Garkuwan Gabas na Katsina.
Bikin nadin ya samu halartar manyan mutane na ciki da wajen jihar, an kuma kammala lafiya.