Sarkin Katsina ya naɗa hakimai da magaddai

Mai martaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir ya naɗa hakimai ukku da kuma magaddai shida a masarautarsa. Bikin naɗin wanda aka yi a fadar sarkin, ya naɗa tsohon Babban Jojin Jihar Katsina Mai Shari’a Saddiƙ Abdullahi Mahuta, wanda aka nada a matsayin sabon Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi. Sai Alhaji Umar Babani Isa Mani wanda aka […]

Sarkin Katsina ya naɗa hakimai da magaddai
Sarkin Katsina ya naɗa hakimai da magaddai

Mai martaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmumini Kabir ya naɗa hakimai ukku da kuma magaddai shida a masarautarsa.

Bikin naɗin wanda aka yi a fadar sarkin, ya naɗa tsohon Babban Jojin Jihar Katsina Mai Shari’a Saddiƙ Abdullahi Mahuta, wanda aka nada a matsayin sabon Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi. Sai Alhaji Umar Babani Isa Mani wanda aka naɗa a matsayin Durɓin Katsina Hakimin Mani.

Su dai waɗannan Hakimai guda biyu na Malumfashi da Mani,dukkansu Hakiman Karaga ne,wato,masu zaɓen sarki. Sai Hakimi na ukkun shi ne Alhaji Abdurrahman Rabi’u, wanda aka naɗa Ɗangaladiman Katsina Hakimin Kafur. Su kuwa Magaddan 6 sun fito daga gundumomi dabam-daban.

Nan take bayan gama naɗa shi,Galadiman Katsian ya naɗa Alhaji Ibrahim “Teacher” a matsayin Sardaunan Galadiman Katsina. Shi dai Alhaji Ibrahim na ɗaya daga cikin na hannun daman Gwamna Masari,kuma ya gaji wannan sarauta a Malumfashi tun daga wajen Kakanni.

Da yake yi musu jawabi bayan kammala naɗe-naɗen, Maimartaba Sarkin ya jawo hankalin wadanda aka naɗa da su maida hankali ƙwarai akan al’amurran da suka shafi al’ummar su tare da tsare musu haƙƙoƙin su da ƙimar su, domin wannan ce kaɗai hanyar tsira a gaban Allah. Ya kuma yi kira ga al’umma baki daya, da a koma ga Allah kuma ayi ta addu’o’i domin samun ɗauki daga Allah Akan larurorin da suka addabe mu, musamman satar dabbobi,yin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane,da sauran su.

Gwamnan Jihar ta Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari kuma mai riƙe da sarautar Dallatun Katsina na daga cikin manyan baƙin da suka halarci wannan bikin naɗin.

Su dai waɗannan naɗe-naɗe masarautar ta maido yinsu a wannan rana ta asabar maimakon daren Salla kamar yadda aka saba,saboda ɗage shagulgulan bikin Salla da masarautar tayi domin nuna alhini da kuma jajantawa akan iftila’in da ya shafi al’ummomin Ƙananan Hukumomin dake fuskantar hare-haren ɓarayin shanu,sata da kuma garkuwa da mutane gami da kisan gilla.