Sarkin Katsina ya nada Sanata Ida Sardaunan Katsina na II

Aranar Asabar 13 ga watan Oktoba bana ne Mai martaba Sarkin Katsina, Dokta Abdulmumin Kabir Usman ya nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin Sardaunan Katsina na II domin maye gurbin marigayi Sufeto Janar Alhaji Ibrahim Commasie. Sanata Ibrahim Ida sanannen dan siyasa ne kuma tsohon ma’aikacin banki kuma dan kasuwa a yanzu. Sanata Ida ya […]

Sarkin Katsina ya nada Sanata Ida Sardaunan Katsina na II

Aranar Asabar 13 ga watan Oktoba bana ne Mai martaba Sarkin Katsina, Dokta Abdulmumin Kabir Usman ya nada Sanata Ibrahim Ida a matsayin Sardaunan Katsina na II domin maye gurbin marigayi Sufeto Janar Alhaji Ibrahim Commasie.

Sanata Ibrahim Ida sanannen dan siyasa ne kuma tsohon ma’aikacin banki kuma dan kasuwa a yanzu.

Sanata Ida ya samu wannan sarauta ce bayan rasuwar Alhaji Ibrahim Commasie wanda shi ne Sardaunan Katsina na Farko a masarautar. An haifi Sanata Ida a cikin garin Katsina a 1949. Bayan kammala karatunsa ya samu aiki a Babban Bankin Najeriya saboda kasancewarsa wanda ya yi karatu a kan abin da ya shafi harkokin kudi. Kafin a nada shi a matsayin Sardauna Katsina, yana rike da sarautar Dan Majen Katsina ne, wadda sarauta ce da aka aro daga masarautar Kano kamar yadda aka ari wannan ta Sardaunan daga Sakkwato. Marigayi Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman ne ya yi masa wannan nadi na Dan Maje.

Sanata Ida ya shiga harkokin siyasa bayan ya ajiye aiki a lokacin marigayi Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’aduwa a lokacin yana Gwamnan Jihar Katsina. Sardaunan Katsina Sanata Ida ya shiga siyasar da kafar dama domin ya yi takarar kujerar Sanata ta shiyyar Katsina kuma ya ci zabe a shekarar 2007, sannan ya samu damar zama Shugaban Kwamitin Harkokin Tsaro, bangaren sojoji a Majalisar Dattawa. Bayan barinsa majalisa, Sanatan ya ci gaba da harkokin kasuwanci hadi da karatu a inda ya halarci Jami’ar Ibadan da Abuja a kokarinsa na karatun digiri na biyu a fannin harkokin kudi.

Kazalika, ba a masarautar Katsina kadai yake rike da sarautar gargajiya ba hatta a kasar Yarabawa ma sai da suka ba shi sarauta. A halin yanzu shi ne “Atuwashe” na masarautar Ikare da ke Jihar Ondo.

Mai martaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmuminu Kabir Usman ne ya ba Sanata Ida wannan sarauta ta Sardaunan Katsina (wadda ke nufin Jagoran Askarawa) a ranar 19 ga watan Yuli na wannan shekarar ta 2018, sannan aka yi bikin nadi a ranar Asabar 13 ga watan Oktoba na 2018.

Sardauna Ida mutum ne wanda ya yi fice ba wai a harkokin siyasa ko kasuwanci ba kadai, hatta a batun bayar da tallafi ga mabukata da kuma son ci gaban ilimi a tsakanin al’umma ba ma kamar ga matasa. Saboda irin tallafa wa ilmin da yake har makarantu biyu aka sanya wa sunansa, daya ta firamare daya kuma ta sakandare.