Sarkin Katsina ya nemi masu ilimi su kama sana’ar hannu
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir ya yi kira ga masu ilimin zamani su rungumi sana’o’in hannu maimakon tsayawa kan aikin gwamnati. Sarkin ya fadi haka ne a jawabinsa na ranar Sallah da na hawan bariki a kofar-Soro da gidan gwamnati.Sarkin ya ya kawo misali da kasar Ingila cewa, in aka ga harkokin da […]
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir ya yi kira ga masu ilimin zamani su rungumi sana’o’in hannu maimakon tsayawa kan aikin gwamnati. Sarkin ya fadi haka ne a jawabinsa na ranar Sallah da na hawan bariki a kofar-Soro da gidan gwamnati.
Sarkin ya ya kawo misali da kasar Ingila cewa, in aka ga harkokin da ake yi sai a yi zaton kamar babu aikin gwamnati. “Za a ga matashi ko magidanci ya dogara da kansa duk da dimbin iliminsa bai tsaya jiran gwamnati ba,” inji shi.
Ya yi kira a sake farfado da makarantun sakandaren koyar da sana’o’i tare da wadata su da kayan aiki. Sai ya yaba da hangen nesan Gwamnan Jihar Ibrahim Shema kan kafa wajen koyar da matasa sana’o’i, inda Sarkin ya ce, yana daga cikin abubuwan da za a rika tunawa da shi.
Sai ya bukaci Musulmi su ci gaba da yi wa Allah godiya kuma su dubi halin da suka shiga a duniya, inda ya ce aikin Hajjin bana kadai ya isa ya zame masu abin alfahari.
Sarki Abdulmumini ya bukaci jama’a su rika kokarin cika alkawari domin abin tambaya ne ranar gobe kiyama. Sai ya jinjina wa kungiyar Kare Muradun Jihar Katsina (KCF) a karkashin jagorancin tsohon Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya Alhaji Ibrahim Commassie da sauran kungiyoyi da suka fito don tallafa wa jihar ta fuskoki da dama.
Da yake maida jawabi, Gwamna Ibrahim Shema ya yi bitar ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a cikin shekara bakwai da ’yan watannin da ya yi yana Gwamna. Ya ba da misali a wajen ilimi cewa ana bayar da shi kyauta, baya ga tura wasu dalibai zuwa kasashen Amurka da Jodan da Sudan da sauransu don koyo fannonin ilimi da gwamnati ke daukar nauyin komai. Kuma ya kuma tabo hanyoyi da kiwon lafiya da noma inda ya ce babu inda gwamnatinsa ba ta yi zarra a kai ba.
Game da zaben 2015, Gwamna Shema ya yi kira a yi zabe cikin lumana, inda ya bayar da misali da yadda aka gudanar da zaben kananan hukumomin jihar cikin kwanciyar hankali.