Sarkin Katsina ya yaba wa Hukumar Kwastam shiyyar Katsina
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya jinjina wa Hukumar Kwastam shiyyar Kaduna da Katsina bisa yadda jami’anta ke gudanar da ayyukansu inda suke dakile ayyukan fasa-kwauri da shigo da jabun magunguna da sauran haramtattun kayayyanki. Sarkin wanda Sa’in Katsina Alhaji Amadu Na-Funtuwa ya wakilta ya fadi haka ne a wurin kona haramtattu […]

Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya jinjina wa Hukumar Kwastam shiyyar Kaduna da Katsina bisa yadda jami’anta ke gudanar da ayyukansu inda suke dakile ayyukan fasa-kwauri da shigo da jabun magunguna da sauran haramtattun kayayyanki.
Sarkin wanda Sa’in Katsina Alhaji Amadu Na-Funtuwa ya wakilta ya fadi haka ne a wurin kona haramtattu da jabun magunguna da hukumar ta kama a Katsina da hukumar a gudanar da hadin gwiwar Hukumar NDLEA.
Sarkin ya ce, ko da rabin wadannan jabu da haramtattun magunguna suka shiga cikin al’umma musamman matasa Allah kadai Ya san irin illolin da za su haifar.
Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shema wanda Kwamishinan Lafiya Alhaji Mannir Talba ya wakilta, bayan jinjina wa hukumar ya tabbatar wa hukumar goyon bayansa tare da yin kira ga jama’a su guji saye tare da shan magani ba da iznin likita ba. Ya ce irin hakan ke janyo lalacewar matasa su zama kauraye ko ’yan fashi da makami da sauran miyagun ayyuka.
Haramtattu da jabun magungunan da kudinsu ya kai Naira miliyan 500 sun hada da maganin karfin maza da na dabbobi da masu sa maye, kuma hukumar ta kama su ne a lokacin da masu fasa kwauri suka yi kokarin shigowa da su ta Jibiya da ke iyakar Najeriya da Nijar.
Kwanturolan Hukumar mai kula da Kaduna da Katsina Yerima Abubakar Gadam ya ce, “Iyakar Jibiya na daya daga cikin iyakokin kasar nan da ake gudanar da fasa-kauri, don haka jami’anmu ke kokari don kawo saukin hakan.”
An kona magungunan da motocin tirela 4 da kanta 2 suka kai filin da ake zubar da shara da ke hanyar Jibiya.