Sarkin Kazaure ya bukaci a kafa cibiyar binciken aikin gona ta Kasa
Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najeeb Hussaini Adamu ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa cibiyar nazarin aikin gona ta kasa wadda sauran cibiyoyin aikin gona za su zama suna karkashin kulawarta. Mai martaba Sarkin ya fadi hakan ne a wajen taron da aka yi da Ministan aikin gona akan matsalolin da suka shafi noma […]
Mai martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najeeb Hussaini Adamu ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kafa cibiyar nazarin aikin gona ta kasa wadda sauran cibiyoyin aikin gona za su zama suna karkashin kulawarta.
Mai martaba Sarkin ya fadi hakan ne a wajen taron da aka yi da Ministan aikin gona akan matsalolin da suka shafi noma da kiwo a Najeriya wanda ministocin Najeriya hudu suka wakilci Gwamnatin Tarayya a birnin Dutse ranar Litinin makon jiya.
Sakin ya ce, samar da cibiyar aikin gonar kwara daya mai inganci zai taimaka wajen samun bunkasar harkokin noma a fadin Najeriya.
Shi kuwa ana sa jawabin Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi koka wa ya yi game da irin halin da cibiyar renon ’ya’yan dabino ta Dutse take ciki. Ya ce, sama da shekaru 35 na kafa cibiyar babu wani ci gaba da aka samu an mayar da cibiyar a matsayin wani wuri na yi wa ma’aikatan da suka yi laifi horo.
Sarkin ya ci gaba da cewar akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta yi bincike mai tsanani akan matsalar cibiyar saboda tun da aka kafa ta zuwa yanzu babu wani abin azo aga ni da cibiyar ta tsinanawa jama’a a jihar Jigawa.
Daga bisani Sarkin ya koka game da yadda babban bankin Najeriya CBN ya baiwa manoman da basu dace ba, saboba da akwai manoman da suka dace a baiwa rancen.
Sarkin ya kuma koka akan irin sharuddan da bankin yake gindaya wa kafin manoma su sami rancen a kungiyance.
Yayin da dan kasuwar nan Alhaji Isah Gerawa damuwarsa ya nuna game da yadda manoman alkama suke fuskantar matsala saboda ’yan kasuwarmu na gida basa satan alkamar da muka noma an anan gida.
Ya ce, rashin satan alkamar daga wajen manoman yasa aka samu koma baya a harkar noman alkamar a Najeriya.
Don haka ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta tallafawa manoman alkamar da kayan aikin noma kamar yadda ake taimaka wa manoman shinkafa.