Sarkin makafin Benin ya bukaci gwamnatoci su tallafa wa nakasassu
Sarkin makafi na Benin, Alhaji Ahmadu Gwaram ya bayyana bukatar a tallafa wa makafi da sauran nakasassu a kasar nan.Alhaji Ahmadu Gwaram ya bayyana bukatar hakan ne kuwa a wata zantawar da ya yi da Aminiya a farkon mako nan, inda ya nemi gwamnatocin tarayya da jihohi kan su tausaya wa nakasassun wajen sama musu […]

Sarkin makafi na Benin, Alhaji Ahmadu Gwaram ya bayyana bukatar a tallafa wa makafi da sauran nakasassu a kasar nan.
Alhaji Ahmadu Gwaram ya bayyana bukatar hakan ne kuwa a wata zantawar da ya yi da Aminiya a farkon mako nan, inda ya nemi gwamnatocin tarayya da jihohi kan su tausaya wa nakasassun wajen sama musu abubuwan more rayuwa don su tafi tare da sauran jama’ar kasa cikin annashuwa da kwanciyar hankali.
Ya ce, “Ina kira da roko zuwa ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, har da kananan hukumomi na kasar nan, a kan su dubi lamarinmu mu makafi da sauran nakasassu, su tausaya mana, su dube mu da idon rahama, su yi mana adalci, su tallafa mana domin mu ma ’yan Najeriya ne kamar sauran mutane.
“Domin, a halin gaskiya, wannan barar da mutane suke gani muke yi, ba da sonmu muke yin ta ba, tilas ce ta sa mu, har muke barin gidajenmu da garuruwanmu, muna kutsawa mu shiga wasu jahohi. Muna yin hakan ne kuwa domin nema wa kanmu abin rufin asiri mu da iyalanmu. Ko da wasu ke cewa wai gwamnati ta tanada mana wuraren koyon sana’a, amma muka ki yarda da shirin, kuma wai da Naira dubu ukku da ake ambata za a biya a wata ga nakasasshe, to don Allah, ko wanda ba shi da mata, yaya wannan kudi zai ishe shi ya rike kansa, balle mai iyali?
A karshe, Alhaji Gwaram ya ce, “Ni abin da na sani, muddin gwamnati ta kama hanyar tallafa mana da gaskiya, nan da wani lokaci mafi yawanmu za mu yi sallama da bara kwata-kwata, mu rungumi sana’a. A cikinmu fa akwai masu ilimin addini da na zamani, amma sai ya kasance larura da rashin gata ta sa muka rungumi bara tamkar sana’a. Ina fata gwamnatoci za su dubi wannan kira nawa, su amsa”.