Sarkin Minna ya fashe da kuka yayin bikinsa na rubu’in karni a sarauta
Ranar Asabar da ta gabata ce Mai martaba Sarkin Minna Alhaji Umaru Faruk Bahago ya fashe da kuka a gaban jama’a inda ya dauki mintoci yana yi abin da ya sa wasu daga cikin jama’arsa musamman wadanda suke masarautar suka bi sawu Sarkin suka rika kuka, wasu idanunsu ya cika da hawaye.Alhaji Umaru Faruk Bahago […]

Ranar Asabar da ta gabata ce Mai martaba Sarkin Minna Alhaji Umaru Faruk Bahago ya fashe da kuka a gaban jama’a inda ya dauki mintoci yana yi abin da ya sa wasu daga cikin jama’arsa musamman wadanda suke masarautar suka bi sawu Sarkin suka rika kuka, wasu idanunsu ya cika da hawaye.
Alhaji Umaru Faruk Bahago ya samu kansa cikin wannan halin ne a filin sukuwar dawaki da ke Minna inda dubban jama’a suka hallara domin kammala bukukuwan cikarsa shekara 25 a matsayin Sarkin Minna.
Daga bisani, Sarkin ya daure ya yi jawabi inda ya yi godiya ga Allah da Ya nuna masa wannan ranar mai cike da tarihi bisa la’akari da babbar nasarar da jama’a suka taimaka masa aka samu wato zaman lafiya a tsakanin mazauna masarautar ba tare da la’akari da addini ko kabila ba.
Ya yi amfani da wannan damar wurin kira ga iyaye su ba gwamnati hadin kai don ta samu nasarar aiwatar da manufofinta da suke da tasiri a rayuwarsu musamman al’amuran da suka shafi ilimi da kiwon lafiya. Kuma ya yi kira ga jama’a su ci gaba da zama da juna lafiya.
Tsohon Shugaban kasa kuma Madakin Minna, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya jinjina wa Sarkin kan gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen hada kan al’ummar masarautarsa wuri daya, duk da kalubalen da aka yi ta fama da su daban-daban a lokuta da dama a kasar nan.Ya ce wannan ne ya sa masarautar ta yi fice, kuma ta zama wurin da kowane dan Najeriya yake muradin zuwa ko zama.
Madakin Minna ya ce bai yi mamaki da wannan babbar nasarar ba, don Sarkin ya gaji kyawawan halayen mahaifinsa ne marigayi Alhaji Ahmadu Bahago wanda ya yi fice wurin wanzar da zaman lafiya da kaunar jama’a ba tare da la’akari da inda suka fito ba.
Gwamnan Jihar Neja kuma Talban Minna, Dokta Mu’azu Babangida Aliyu kira ya yi a samar wa sarakuna matsayi a kundin tsarin mulki da ake yi wa gyarar fuska don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali kamar yadda suka yi kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.
Talban ya nuna rashin dacewa game da irin rikon sakainar kashin da ake yi wa iyayen kasar da inda ya ce ba a nemansu sai an rasa inda za a sa kai a kasar nan.
A watan Maris din 1988 ne Gwamnan Jihar Neja Birgediya Janar Lawan Gwadabe ya tabbatar da nada Alhaji Umar Bahago a matsayin Sarkin Minna, bayan da ya yi takara da wadanda suka nuna sha’awarsu daga Gwarawan Bosso da Paiko.