Sarkin Musulmi ga Gwamnatin Tarayya: A ceto makarantun allo

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta ceto makarantun allo daga durkushewar da suka yi. Ya bukaci haka ne a lokacin bikin yaye dalibai na Jami’ar Nile da ke Abuja a ranar Asabar da ta gabata.Ya ce: “Shehu Usman danfodiyo ya rubuta littattafai kusan 300 a fannonin ilimi daban-daban da […]

Sarkin Musulmi ga Gwamnatin Tarayya: A ceto makarantun allo
Sarkin Musulmi ga Gwamnatin Tarayya: A ceto makarantun allo

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta ceto makarantun allo daga durkushewar da suka yi. Ya bukaci haka ne a lokacin bikin yaye dalibai na Jami’ar Nile da ke Abuja a ranar Asabar da ta gabata.
Ya ce: “Shehu Usman danfodiyo ya rubuta littattafai kusan 300 a fannonin ilimi daban-daban da suka hada da Tauhidi da Fikhu da zamantakewar rayuwa, don haka ya kamata jama’a su nemi ilimi. Na kadu sosai da na karanta labarin cewa fiye da yara miliyan 10 ne ba sa zuwa makaranta a Najeriya, wannan abin damuwa ne. A yanzu da ’yarmu Ministar Ilimi take tare da mu a wurin taron nan, ya kamata ta sanar da Shugaban kasa don a ceto halin da ilimi ya samu kansa a ciki, musamman ma makarantun allo da a yanzu suke cikin mawuyacin hali.”
Ya nemi jama’a su kasance masu hakuri da juna, kuma su fahimci tashin hankali ba zai haifar wa kasar nan da mai ido ba, inda ya nemi jama’a su rika tattauna duk wata matsala cikin ruwan sani don a samu maslaha maimakon su dauki doka a hannunsu.
Jami’ar ta yaye dalibai 45 wadanda suka hada daga tsangayar tsare-tsare kan kasuwanci da tsimi da tanadi da ilimin Chemistry da kuma kimiyyar kwamfuta.
dalibai hudu ne suka fita da digiri mai daraja ta daya, wadanda suka hada da Isma’il Isa Modibbo daga tsangayar Kimiyyar Kwamfuta da Ngele Anthonia Nnebuife daga tsangayar tsare-tsare kan kasuwanci da Habib Babatunde Ibikunle daga tsangayar tsimi da tanadi da kuma Muhammad Bello Ibrahim daga tsangayar Koyar da Chemistry, inda kuma Isma’il Modibbo ya zama gwarzon shekara bayan ya samu maki 4.72.