Sarkin Musulmi ga Gwamnonin Arewa:

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya shawarci gwamnonin Arewa su daina rabewa da sunan Sardauna Ahmadu Bello, maimakon haka kamata ya yi su riqa yin aiki irin na Ahmadu Bello tare da nuna gaskiya a yayin gudanar da ayyukansu.“ Lokaci ya yi da za mu daina rabewa a inuwar Sardauna, dole ne mu fito mu fara […]

Sarkin Musulmi ga Gwamnonin Arewa:
Sarkin Musulmi ga Gwamnonin Arewa:

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya shawarci gwamnonin Arewa su daina rabewa da sunan Sardauna Ahmadu Bello, maimakon haka kamata ya yi su riqa yin aiki irin na Ahmadu Bello tare da nuna gaskiya a yayin gudanar da ayyukansu.
“ Lokaci ya yi da za mu daina rabewa a inuwar Sardauna, dole ne mu fito mu fara koyi da irin kyawawan halayensa. Qalubale ga gwamnoninmu shi ne sun zo a lokacin da tattalin arzikin duniya da qasar nan ke cikin wani hali. Ga kuma matasanmu da yawa da ba su da aikin yi. Saboda haka akwai buqatar ku duba hanyayoyin da za a bi wajen samar wa matasanmu aikin yi domin su samu abin dogaro da kansu,”inji shi.
Sarkin ya yi wannan gargadin ne a yayin da yake jawabi a wurin taron cika shekara 50 da kashe Sardauna da Abubakar Tafawa balewa, wanda Gidauniyr Sardauna ta shirya kuma aka gudanar jiya alhamis a Kaduna.
 A nasa tsokacin,tsohon  Shugaban kotun daukaka qata ta tarayya Mai Shari’a Mamman Nasir, wanda ministan shari’a  ne a gwamnatin Sardauna, ya bayyana  Wadanda suka kashe tsohon Firimiyan Arewa kuma Sardauna Sakkwato Ahmadu Bello shekaru 50 da suka wuce a matsayin maqiyan Najeriya.
A cewarsa, mutanen da suka kashe shi ba su da wata hujjar yin haka, domin marigayi Sardauna mutum ne na kowa da kowa.
Ya ce akwai buqatar shugabannin qasar nan, musamman ‘yan yankin Arewa su tabbatar  sun koyi halayen marigayin. “ A yau ban zan iya cewa komai ba, saboda a rana irin ta yau ne aka halaka shugabanmu Firimiyan Arewa Ahmadu Bello da maqiyan qasar nan suka yi. Kuma ba su da wata hujjar yin haka, domin shi na kowa da kowa ne a qasar nan,” inji shi.
A nasa saqon, Shugaban qasa Muhammadu Buhari, wanda Gwamnan jahar Kadun, Nasir El-Rufai ya wakilta, cewa ya yi a shirye yake ya kare martabar qasar nan.Ya kuma yaba wa jajircewar  da Shugabannin qasar nan da kuma na Arewa suka yi wajen gabatar da shugabanci nagari domin daukaka martabar jama’arsu. “ Idan shugaba ya tafiyar da mulkinsa cikin tsoron Allah da gaskiya, ko da ya rasa ransa jama’a za su tuna da shi,” inji shi.
Shugaban ya yaba wa  su marigayayi Sardaunan Sakkwato da Tafawa balewa da sauransu, tare da yin addu’ar Allah Ya jiqansu da rahamarSa.
Shi kuwa danmatsanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule, wanda shi ne babban baqo mai jawabi, ya bayyana Ahmadu Bello ne a matsayin shugaba mai tsoron Allah, wanda kuma babu ruwansa da nuna qabilanci a mulkinsa.
Ya ce Sardauna shugaba ne da ya dauki duk wani dan Arewa a matsayin dan Arewa ba kuma tare da nuna wani bambancin addini ko qabilanci ba, wanda hakan ya sa duk jama’ar yankin suke kallon kansu a matsayin tsinsiya madaurinki daya.
A nasa jawabin,Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, gargadi ya yi ga masu neman bata sunayen su Sardauna da Tafawa balewa da sauran mutanen kirki da aka kashe a lokacin juyin mulki na farko a shekarar 1966, inda ya ce ya kamata su sani cewa, mutanen Arewa a shirye suke su kare martabar wadannan shugabbanin nasu da aka kashe.