Sarkin Musulmi ga mata: Kada ku karbi kudin sata daga mazajenku
Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci mata Musulmi su kasance wani bangare na yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar kin karbar kudin sata daga mazajensu ma’aikata ko wadanda suke rike da mukaman gwamnati.Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya kuma […]

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci mata Musulmi su kasance wani bangare na yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar kin karbar kudin sata daga mazajensu ma’aikata ko wadanda suke rike da mukaman gwamnati.
Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya kuma bukaci matan gwamnoni da na sarakuna su jagoranci yekuwar bai wa ’ya’ya mata ilimi.
Alhaji Sa’adu Abubakar ya bayyana haka ne a wajen babban taron shekara-shekara na kungiyar Mata Musulmi ta kasa (FOMWAN) karo na 30 da aka gudanar a Ilori da ke Jihar Kwara.
Taron mai taken: “Iyaye Mata da Jagoranci,” wanda aka gudanar a ranar Juma’ar makon jiya, Sarkin Musulmi wanda shi ne jagoran sarakunan kasar nan, ya ce dimbin matsalolin da suke damun kasar nan “suna farowa ne daga gidajenmu.”
Ya ce idan Najeriya tana bukatar ta ga canji a tsakanin ’ya’yanta kamar yadda take nuna sha’awar hakan a yanzu, wajibi ne mata su fara wa’azin yaki da cin hanci da rashawa daga gidajensu.
Ya kuma ce wajibi ne ’yan Najeriya su zauna a shirye wajen canja kansu kamar yadda suka zabi canjin a zaben Shugaban kasa da ya gabata.
“Wajibbi ne mata su rika tattauna batun cin hanci da rashawa, su rika tambayar mazajensu daga ina suke samun haramtacciyar dukiyarsu musamman matan ma’aikata ko jami’an gwamnati. Idan kuka lura bayan ’yan watanni da kasancewar mazajenku ma’aikata ko mukarraban gwamnati sun fara sayen motoci masu dan karen tsada, suna gina gidaje ko’ina barkatai ku tuhume su a ina suke samun wadannan kudi dare daya.”
Sarkin Musulmi ya kara da cewa: “A matsayinku na mata, wajibi ne ku ku rika tsoma baki kan matsalolin da suke addabar kasar nan, ku tsara manufofin da za su sanya duk wanda ke neman wani mukami ya saurare ku, ko da ba zai ji dadin abin da kuke fada ba.”
Sarkin Musulmin ya nanata bukatar da ke akwai ga mata su sauke nauyinsu na tarbiyyantar da yara da kula da jin dadin jama’a.
“Idan ba mu samu kyakkaywar al’umma ba wadda yara za su taso da tsoron Allah, zan iya cewa ba mu da al’umma,” inji Sarkin Musulmin.
A jawabin Gwamnan Jihar Kwara Alhaji Abdulfatah Ahmed lokacin bude taron ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ba ta cin gajiyar dimbin albarkatun kabilu da jama’a da Allah Ya hore mata wajen mayar da kasar nan cikakkiyar kasa.
Ya ce bambance-bambance addini da kabila da Allah Ya albarkaci kasar nan, kamata ya yi a yi amfani da su wajen bunkasa kasar nan don ta ci gaba.
A jawabin babban bako Dokta AbdulRauf Wale Babalakin ya nuna gudunmawar da iyaye mata za su iya bayarwa ne wajen renon ’ya’yansu.
Ya ce, “bai dace a haifi mutum ya taso a hannun iyaye marasa tarbiyya ba. Kuma tauye masa ’yancinsa na yaro ne, a ce mutane da suka rene shi ba su yi taka-tsantsan wajen yin abin da ya dace da shi ba.”
A jawabin maraba shugaban taro Mai shari’a Mustapha Akanbi ya yi kira ga daukacin Musulmi su hada kai wajen la’antar ayyukan ta’addanci da wasu masu fakewa da addinin Musulunci suke aikatawa.
Ya jawo ayoyi daga Alkur’ani Mai girma domin kafa hujja, inda Mai shari’a Akanbi ya ce kiran mutane zuwa ga Musulunci bai kamata ta hanyar barazana da tashin hankali ba, maimakon haka ya zamo ta hanyar nuna kyawawan dabi’un Musulunci ga wadanda ba Musulmi ba.
Mai shari’a Akanbi wanda Dokta Mudashir Abdulsalam ya wakilta ya ce, “Wajibi ne kungiyoyin dukkan addinai su yi kokarin fahimtar sauran addinan bayan nasu domin hada hannu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a matsayin Najeriya na kasa mai addinai da yawa.”
Ya bukaci Musulmi su yi watsi da “mugun kulli da son zuciya da hadama da kyamar juna” a tsakaninsu, yayin da ya bukaci shugabannin siyasa su guji cusa gaba a tsakanin mabiya addinai.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi Hajiya Maryam Yakubu Ikunaiye wadda shugabar wata kungiyar yada kyawawan dabi’u na shugaban kasa Muhammadu Buhari ne wato Buharian Culture Organisation, a kan bayanin na Mai alfarma Sarkin Musulmi, ta ce: “Na gamsu da bayanin Mai alfarma Sarkin Musulmi da ya ce mace na iya tagazawa wajen hana mijinta handamar dukiya. Wasu matan na dora wa mazajensu abin da suka san albashinsu ba zai iya samarwa ba, wanda hakan na iya jefa su ga handamar dukiyar da ba su mallaka ba.”
Ta kara da cewa: “Wani zubin kuma mazajen ne a radin kansu ke barnata dukiya inda za ka ga mutum guda ya mallaki tarin gidaje da motoci inda wani sai ya yi wata shida bai shiga wata motar ba.”
Ta ce, idan mace ta guji dora wa mijinta nauyin da ya fi karfinsa, ko idan ya yi hakan a radin kansa ta nuna masa ba daidai ba ne, hakan na iya tasiri ya guji aikata hakan, “Wannan na daga cikin manufar kungiyarmu ta yada kyawawan manofofin Shugaban kasa wanda kamar yadda kowa ya yi masa shaida bai da halin handama bare ya yi barna,” inji ta.