Sarkin Musulmi ga Tambuwal: Ka hana bara a titunan Sakkwato
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi kokarin hana bara a kan titunan birnin Sakkwato ganin yadda mabarata suka cika garin.Shi kuma Gwamnan ya roki malaman addini da ke jihar da su yi wa’azi don wayar da kan jama’a su ji tsoron Allah […]
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi kokarin hana bara a kan titunan birnin Sakkwato ganin yadda mabarata suka cika garin.
Shi kuma Gwamnan ya roki malaman addini da ke jihar da su yi wa’azi don wayar da kan jama’a su ji tsoron Allah su daina barar.
Sarkin Musulmi da Gwamna Tambuwal sun yi wadannan kalamai ne a ranar Asabar da ta gabata, lokacin rabon kayan masarufi na fiye da Naira miliyan 157 da Kwamitin Zakka da Wakafi na Jihar ya raba wa mabukata. Sun ce wannan kira na A daina bara abu ne mai muhimmanci da ya shafi jihar.
Gwamna Tambuwal ya ce wajibi ne ga malamai su yi wa’azi kan bara a kan hanyoyin mota da wuraren zaman al’umma don hakan yana jefa Musulmi da Musulunci a cikin mawuyacin hali.
Gwamna Tambuwal ya kara da cewa yawon bara na daya daga cikin abin da ke kara jefa al’umma shiga miyagun halaye don haka ya bukaci iyaye su samar da tarbiyya da ilimi ga ’ya’yansu.
Sai ya yi alkawarin taimaka wa kwamitin don ya cimma burin da aka kafa shi.
Gwamnan ya bukaci Musulmi su rika fitar da Zakka da wakafi kamar yadda addini ya shardanta don samar da zaman lafiya da walwala cikin jama’a.
Sarki ya kara kiran a taimaka wa marayu da zawarawa da marasa karfi kan wannan ya bukaci kungiyar Gwamnonin Arewa su taimaki al’ummar Arewa maso Gabas da yakin Boko Haram ya daidaita. Kuma ya gode wa Mista Eric kan kokarin da ya yi na taimakon jama’ar Musulmi da shinkafa da tumatir da alkawarin gina masallacin Juma’a biyu kan Naira miliyan goma, duk da ba Musulmi ba ne.
Kayan da aka raba sun hada da buhu 100 na shinkafa da keken dinki 100 da katifa 50 kwalin tumatur din gwangwani dubu uku da firiza 20 da sauransu.