Sarkin Musulmi: Ka dinga bincike kafin yin tsokaci — Gwamna Aliyu ga Shettima

Shettima ya gargaɗi gwamnatin Sakkwato kan yunƙurin tsige Sarkin Musulmi.

Sarkin Musulmi: Ka dinga bincike kafin yin tsokaci — Gwamna Aliyu ga Shettima

Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta buƙaci mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da ya riƙa bincike kafin ya yi tsokaci kan al’amuran da suka shafi ƙasa baki ɗaya.

Da take mayar da martani kan gargaɗin da Shettima, ya yi a wanen taron tsaro na yankin Arewa Maso Yamma da aka yi a Jihar Katsina a ranar Litinin.

Gwamnatin ta ce kamata ya yi mataimakin shugaban ƙasar ya tuntuɓi gwamna Ahmed Aliyu, domin tabbatar da sahihancin labarin kafin yin magana kan batun tsige Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar a bainar jama’a.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna Aliyu, Abubakar Bawa ya sanyawa hannu, gwamnatin ta buƙaci mataimakin shugaban ƙasar da ya zamana mai sanin al’amuran da suka shafi ƙasa baki ɗaya kafin yin tsokaci a kansu.

“Gaskiya mun yi tsammanin Mataimakin Shugaban Ƙasa zai tuntuɓi Gwamna kafin yin magana a fili.

“A matsayinsa na dattijo kuma uba ga kowa, ya kamata yake bin diddigin abu kafin ya yanke hukunci a kan batun da wasu marasa kishi suka yaɗa a shafukan sada zumunta.

“Gaskiyar magana ita ce babu wani yunƙuri na tsige Sarkin Musulmi, kuma babu wata barazana da muka yi masa dangane da hakan ba.

“Sultan yana samun ikon da duk yake da buƙata. Ba mu taɓa daƙile wani ’yancinsa ko haƙƙinsa ba.

“Don haka ba ma buƙatar a ce mu kare ko yaɗa Sarkin Musulmi ba. Aikinmu ne.

“Gwamnati da jama’ar Sakkwato suna girmama majalisar sarakuna kuma za su ci gaba da yin haka. Don haka gwamnati tana tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa, za ta ci gaba da kare majalisar Sarkin Musulmi da mutuncinta a kowane lokaci,” in ji sanarwar.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya