Sarkin Musulmi ne na 18 cikin Musulmin da suka fi fada a ji a duniya

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ne mutum na 18 da suka fi fada a ji a tsakanin Musulmin duniya.Wannan kyakkyawan labari yana kunshe ne a cikin kundi na biyar na Mujallar Musulmi 500, wadda kamar wata kundi ne na tara bayanan Musulmin da suka fi fada a ji a duniya, na shekarar 2013 […]

Sarkin Musulmi ne na 18 cikin Musulmin da suka fi fada a ji a duniya
Sarkin Musulmi ne na 18 cikin Musulmin da suka fi fada a ji a duniya

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ne mutum na 18 da suka fi fada a ji a tsakanin Musulmin duniya.
Wannan kyakkyawan labari yana kunshe ne a cikin kundi na biyar na Mujallar Musulmi 500, wadda kamar wata kundi ne na tara bayanan Musulmin da suka fi fada a ji a duniya, na shekarar 2013 da 2014.
Abdallah Schleifer, wani farfesa kuma babban masani a cibiyar harkokin talabijin da aikin jarida a zamanance ta Kamal Adham Centre for Telebision & Digital Journalism a Jami’ar American Unibersity da ke Alkahira ta kasar Masar wanda ya rubuta gabatarwa a kan bugun na bayan nan, ya ce akwai Musulmi biliyan daya da miliyan 700 a duniya a yau, wato kimanin kasha 23 cikin 100 na jama’ar duniya ko daya bisa biyar na jama’ar duniya.
“A matsayinsu na ’yan kasa a kasashensu mabambanta; amma suna jin su al’umma guda ne al’ummar Musulmin duniya,” kamar yadda Farfesa Schleifer ya fadi a cikin mujallar da aka zabi masu fada-ajin.
Kuma ya ce, mujallar takan gano fada a jin da wasu Musulmi ke da shi a tsakanin jama’arsu ko a madadin jama’arsu.
Ya ce fada a jin ya kunshi duk wani mutum da yake da iko ko mulki (a al’adance ne ko a akida ko dukiya ko siyasa ko wani abu daban) da zai iya kawo canjin da zai yi tasiri a duniyar Musulmi.
Ya ce, tasirin yana iya zama mai amfani ko akasainsa, ya danganta ga fahimtar kowane mutum. Kuma ya kara da cewa, fada ajin kan iya kasancewa ta addini kamar malami ya rika wa’azi ko huduba ko karantarwa yana tasiri a imaninsu ko fahimta ko dabi’unsu, ko kuma kan iya kasancewa wani shugaba da ke kawo sauyi a harkokin rayuwa da tattalin arziki da suka shafi rayuwa ko kuma wani mai fasaha da ke iya inganta wata fitacciyar al’adarsu.
Mujallar ta zabi Sarkin Musulmi ne kan kyakkyawan shugabancinsa a harkokin addini a Najeriya.
Ta ce, Sarkin Musulmi yana da matukar tasirin fada a ji a matsayinsa na shugaban Majalisar koli kan Harkokin Addinin Musulunci, kuma a matsayina na Sarkin Musulmi ana daukarasa a matsayin shugaban addinin Musulunci a Najeriya mai Musulmi miliyan 74 da dubu 600, da suka haura kasha 50 cikin 100 na jama’ar kasar nan.
Mujallar ta yaba wa Sarkin Musulmin kan kokarinsa na kwantar da kurar gaba a tsakanin Musulmi da Kiristoci da bullo da hanyoyin dakile tasirin Boko Haram, ciki har da gayyatar Majalisar Tattauna tsakanin Musulmi da Kirista ta duniya zuwa Najeriya.
An fara buga mujallar ce a shekarar 2009, kuma ta bana cibiyar Royal Islamic Strategic Studies Centre Amman, Jordan, da hadin gwiwar cibiyar fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista ta Yarima Al-Waleed Bin Talal Centre for Muslim-Christian Understanding da ke Jami’ar Georgetown Unibersity a Amurka suka buga ta.
Babban Shehin Jami’ar Al-Azhar kuma Babban Limamin Masallacin Al-Azhar Sheikh Ahmad Muhammad Al-Tayyeb, Musulmi mafi tasiri a shekarar 2013/2014. Sai Sarki Abdullah bin Abdul’Aziz Al-Saud, na Saudiyya, sai Ayatollah Hajj Sayyid Ali Khamenei, na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke bi masa, sai kuma Sarki Abdullah II bin Al-Hussein na Jordan.