Sarkin Musulmi ya bukaci Gwamnati ta rika karrama mahaddata
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta rika karrama mahaddata Alkur’ani don bunkasa musabakar Alkur’ani da suke wakiltar kasar nan a yayin gudanar da gasar musabaka ta duniya. Sarkin Musulmi ya bukaci haka ne lokain bude babban taron kasa kan musabaka da Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usman dan […]
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta rika karrama mahaddata Alkur’ani don bunkasa musabakar Alkur’ani da suke wakiltar kasar nan a yayin gudanar da gasar musabaka ta duniya.
Sarkin Musulmi ya bukaci haka ne lokain bude babban taron kasa kan musabaka da Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usman dan Fodiyo ta shirya a shekaranjiya Laraba.
Cibiyar ce ke shiryawa da daukar nauyin gudanar da gasar musabaka ta kasa.
“Ina kira ga Gwamnatin Tarayya ta rika karrama mahaddata kur’ani wannan shi ne zai bunkasa kasar nan da tsima wasu matasan Musulmi su dauki addininsu da girma,” inji shi.
Sarkin Musulmin wanda Alhaji Muhammad Bello Abubakar Ubandoman Hamma’ali ya wakilta ya jinjina wa cibiyar kan karbar littafan jihadin Shehu dan Fodiyo da ta yi inda take tace su da fassarawa da bugawa tare da raba su ga jama’a.
Ya ce, wannan hobbasa tasu ya sanya kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta buga kusan littattafai 100 kan ayyukan jagororin jihadin ta hanyar taimakon ma’aikatan cibiyar, “Amma yanzu mun yi la’akari da wasu gyare-gyare da za a yi a bugun littattafan na gaba, kan haka nake kira ga jama’ar Musulmi su taimaka wa wannan cibiya da duk abin da take bukata don ciyar da addini gaba a kasar nan,” inji Sarkin Musulmin.
A jawabin Gwamnan Jihar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal wanda Shugaban Ma’aikata na Jihar Alhaji Mujtaba Ahmad ya wakilta ya gode wa mahalarta taron, inda ya ce gwamnatinsa za ta ba cibiyar taimakon da ya dace don ciyar da addini gaba.
A jawabin maraba, Shugaban Jami’ar Farfesa Abdu Zuru ya tabo tarihin musabakar ce da kuma ayyukan da Sashin Nazarin Addinin Musulunci ke gudanarwa da suka hada da karantarwa da gudanar da gasar musabaka don zakulo gwanayen karatun kur’ani zuwa gasar ta duniya da bincike da shirya tarurruka kan addini da sauransu.