Sarkin Musulmi ya ce a duba sabon watan Rabi’ul sani

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmi da su fara dubar jinjirin watan Rabi’ul sani 1442AH daga ranar Lahadi. Sarkin Musulmi ya fitar da bayanin hakan ne ta hannun Shugaban Kwamitin Ganin Wata na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu. An kubutar da matashi baya awa bakwai a cikin kwata Hadimin […]

Sarkin Musulmi ya ce a duba sabon watan Rabi’ul sani

Wata

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmi da su fara dubar jinjirin watan Rabi’ul sani 1442AH daga ranar Lahadi.

Sarkin Musulmi ya fitar da bayanin hakan ne ta hannun Shugaban Kwamitin Ganin Wata na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu.

“Ina sanar da al’ummar Musulmi su fara duba watan Rabi’ul Sani a gobe Lahadi daidai da 29 ga watan Rabi’ al-awwal 1442AH.

“Duk Musulmin da ya ga wata ya sanar da basaraken da ke kusa da shi domin sanar da Majalisar Sarkin Musulmi”, sanarwar.

Watan Rabi’us Sani shi ne wata na hudu a kalandar Musulunci wanda ke shekara ta 1442 Bayan Hijira.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa