Sarkin Musulmi ya ce rashin adalcin shugabanni ke jawo rashin tsaro a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar ya ce rashin adalcin shugabannin Najeriya ne ya jefa kasar nan cikin halin rashin tsaro da kwanciyar hankali. Ya ce da shugabanni na tafiyar da mulkinsu yadda ya kamata da kasar ba ta samu kanta a cikin wannan matsalar rashin tsaro ba.Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a […]

Sarkin Musulmi ya ce rashin adalcin shugabanni ke jawo rashin tsaro a Najeriya
Sarkin Musulmi ya ce rashin adalcin shugabanni ke jawo rashin tsaro a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad AbubakarMai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar ya ce rashin adalcin shugabannin Najeriya ne ya jefa kasar nan cikin halin rashin tsaro da kwanciyar hankali. Ya ce da shugabanni na tafiyar da mulkinsu yadda ya kamata da kasar ba ta samu kanta a cikin wannan matsalar rashin tsaro ba.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a wurin taron kasa na malamai da sarakuna kan rawar da za su taka wajen samar da zaman lafiya da hadin kai da tsaro a kasar nan wanda aka gudanar a Kaduna.
“Rashin adalci ne ya janyo rashin tsaro a kasar nan. Da shugabannin kasar nan suna yin abin da ya dace da ba mu shiga cikin matsala ba. Al’amura da yawa ba su tafiya yadda ya kamata saboda shugabannin ba su son hakan. A kullum al’amura kara tabarbarewa suke yi a kasar nan,” inji shi. Ya kara da cewa, “A matsayinmu na shugabannin Musulmi mun san abin da Allah Ya ce game da shugabanci. Muna sane da yadda Annabinmu ya ba da rayuwarsa domin mu yi koyi da shi sannan na yi imani idan har za mu bi abin da Alkur’ani ya ce da kuma kyawawan dabi’un Annabinmu ba za mu kauce ba.”
Sarkin Musulmi ya shawarci malamai kan sun yi kokari wajen tsokaci da kuma bayyana halayyar ’yan kungiyar Boko Haram da dabi’unsu cewa ba Musulunci ba ne.
“Malamai da sarakuna sun yi kokari wajen gabatar da kasidu da ke nuna cewa dabi’un wadannan ’yan kungiya ya kauce wa Musulunci. Malamai dai ba suke da mulki ba, sarakuna ba su ke da gwamnati ba. Abin da kawai za su iya yi shi ne su ba shugabanni shawara kuma muna yin hakan ba tun yau ba, a kan yadda za a magance matsalar,” inji shi.
Ya ce “Idan akwai zaman lafiya a tsakanin Musulmi wadanda mu muka fi yawa a kasar nan za a samu dauwamammen zaman lafiya a kasa. Sannan idan akwai zaman lafiya za a samu ci gaba a kasa. Zan iya cewa akwai dalilai masu yawa a kan abin da ke faruwa a yankin Arewa, kila Allah na son mu canja halayenmu ne. Saboda haka lokaci ya yi da za mu zauna domin tattauna matsalolin da ke damunmu a matsayinmu na Musulmi. Kuma malaman da suka halarci wannan taro daga sassan kasar nan domin zama a karkashin lema daya abin a yaba ne.”
Sarkin Musulmin ya bukaci malaman su ci gaba da yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya inda ya ce da addu’arsu da na sauran bayin Allah, sai Allah Ya kawo karshen wadannan matsalloli da suka addabi Arewa da kasa baki daya.
Sauran wadanda suka yi jawabai a wurin taron sun yi kira ne ga malamai, musamman wadanda za su gudanar da tafsir a azumin bana, kan su kaurace wa yin amfani da kalaman suka ga junansu.