Sarkin Musulmi ya kaddamar da fara jigilar maniyyata a filin jirgin saman Kebbi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya kaddamar da tashin jirgin farko na maniyyata aikin Hajjin bana daga sabon filin jirgin sama na Sa Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi.Kimanin maniyyata 530 suka tashi a jirgin Mad Air mai lamba 5N-BMA wanda ya kwashe su zuwa Saudiyya. Da yake jawabi yayin kaddamarwar Alhaji Sa’ad […]

Sarkin Musulmi ya kaddamar da fara jigilar maniyyata a filin jirgin saman Kebbi
Sarkin Musulmi ya kaddamar da fara jigilar maniyyata a filin jirgin saman Kebbi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya kaddamar da tashin jirgin farko na maniyyata aikin Hajjin bana daga sabon filin jirgin sama na Sa Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi.
Kimanin maniyyata 530 suka tashi a jirgin Mad Air mai lamba 5N-BMA wanda ya kwashe su zuwa Saudiyya.
Da yake jawabi yayin kaddamarwar Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi kira ga maniyyatan su dukufa wajen yi wa wannan kasa addu’ar samun zaman lafiya. Kuma ya bukaci su kasance masu bin doka da oda tare da zama wakilan Najeriya nagari a yayin zamansu a kasa Mai tsarki don gudanar da aikin Hajjin bana.
Sarkin Musulmin ya ce sakamakon yanayin da duniya ta tsinci kanta a ciki na barkewar cutar Ebola, wajibi ne kowane maniyyaci ya tabbatar da cewa an tantance shi ta hanyar gwajin jami’an lafiya a nan Najeriya da kuma kasa Mai tsarki domin samun nasarar aikin Hajjin bana.
Sai ya yi kira ga jami’an kasar Saudiya su hanzarta ba da biza ga maniyyatan kasar nan domin a samu kwashe su a cikin lokacin da Saudiyya ta dibar wa Najeriya.