Sarkin Musulmi ya nemi a dauki nauyin marayun da Boko Haram suka kashe wa iyaye
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga masu hannu da shuni da sarakunan kasar nan su dauki nauyin yaran da Boko Haram ta kashe wa iyaye, musamman a jihohin Borno da Yobe da sauran jihohin Arewa maso Gabas. Sarkin Musulmi ya yi wannan kira ne a makon jiya a wurin […]

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira ga masu hannu da shuni da sarakunan kasar nan su dauki nauyin yaran da Boko Haram ta kashe wa iyaye, musamman a jihohin Borno da Yobe da sauran jihohin Arewa maso Gabas.
Sarkin Musulmi ya yi wannan kira ne a makon jiya a wurin kaddamar da littafiin sharhin Iziya (Fath Rabbil Bariyyah), wanda Dokta Muhammad Mansur Sakkwato ya rubuta.
Ya ce a yanzu akwai marayu sama da dubu 50 a sansanonin’yan gudun hijira da ke Arewa maso Gabas da ya kamata masu kudi su kai wa dauki. “Marayun nan da suka rasa mahaifansu kan tada kayar baya da ’yan ta’adda suka yi, suna bukatar taimako na gina rayuwarsu don su zama masu amfani a cikin al’umma. Mun yanke shawara lokacin da muka yi zaman tattaunawa cewa kowace masarauta akalla za ta dauki nauyin yara 5 ta kula da su don su amfani kansu da al’umma da kasa baki daya,” inji Sarkin Musulmi.
Ya yi kira da babbar murya ga masu kudin kasar nan da su yi koyi da hamshakin dan kasuwar nan, Alhaji Umarun Kwabo da ya dauko marayu 150 don kulawa da su a wata makaranta da ya gina a Sakkwato. Ya kuma gode wa marubucin littafin da aka kaddamar, inda ya ce abin a yaba ne kuma littafin zai kara taimakon masu neman ilimi don bin hanyar da ta dace.
Malamin da ya yi bitar littafin, Sheikh Aminu Daurawa ya yi kira ga malamai su sanya littafin cikin zaurukan karantarwarsu da ajujuwan dalibai don karantar da su. Ya ce hakan na da mutukar muhimmanci.
A wurin bikin an tara sama da Naira miliyan 43. Gwamnatin Jihar Sakkwato ce ta ba da gudunmawa mafi tsoka ta Naira miliyan 12.