Sarkin Musulmi ya nemi a kawo karshen matsalar tsaro a Arewa

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci a kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin Arewa inda ya nuna matukar damuwa game da halin rashin tsaro ke ciki a yankin.Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wurin rufe gasar karatun Alkur’ani ta kasa da aka gudanar […]

Sarkin Musulmi ya nemi a kawo karshen matsalar tsaro a Arewa
Sarkin Musulmi ya nemi a kawo karshen matsalar tsaro a Arewa

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci a kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin Arewa inda ya nuna matukar damuwa game da halin rashin tsaro ke ciki a yankin.
Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wurin rufe gasar karatun Alkur’ani ta kasa da aka gudanar a Dutse Jihar Jigawa, inda ya ce Arewa ta tasam ma lalacewa saboda halin da ta samu kanta a ciki na rashin tsaro da harkar Boko Haram ta haifar da kuma matsalar ’yan fashi da barayin shanu da rikicin Fulani makiyaya da
manoma, inda ake amfani da wata dama a shiga rigar siyasa ana kashe rayukan jama’a ba su san hawa ba balle sauka.
Sai ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta daukar matakin samar da zaman lafiya a daukacin jihohin Arewa, kuma ya shawarci jama’ar Arewa su mike tsaye sosai wajen
taimakawa a samu tsaro a yankin.
Ya ce wani abin takaici da ban haushi, shi ne gidajen da ake konawa da kayan da ake konawa da mutanen da ake kashewa duk na ’yan Arewa ne babu wani dan wata kabila da ake kashewa ko ake lalata masa dukiya.
Sarkin Musulmi ya ce ’yan Boko Haram da barayi da ’yan siyasar da aka bata wa rai, duk kamata ya yi gwamnati ta samar da hanyoyin da za a daidaita da su, “barayi a yi musu
wa’azi su daina, gwamnatin ita ta san hanyoyin da za ta bi wajen samar da sulhu da kowa amma rayuwa a yankin Arewa ta zama wata iri ba kamar yadda aka saba a baya ba.
A bana Jihar Kaduna ce ta yi nasarar cinye gasar masabakar ta kasa, inda wakilanta suka koma gida da kyaututtukan motoci da kujerun Hajji.