Sarkin musulmi ya sanar da ganin watan Sallah a Najeriya

Gobe Juma’a ce ranar Idin Sallah karama.

Sarkin musulmi ya sanar da ganin watan Sallah a Najeriya

Muhammad Sa’ad Abubakar III, Sarkin Musulmin Najeriya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.

Hakan ya tabbatar da ranar Juma’a, 1 ga watan Shawwal ta shekarar 1444 Bayan Hijira a matsayin ranar Idin Sallah karama.

Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce an tabbatar da sahihancin ganin watan a wurare da dama a fadin kasar.

Ya bukaci musulmi da su ci gaba da kasancewa jakadu na zaman lafiya da kowa ba tare da nuna wani bambanci a tsakanin al’umma ba.

Ya yi addu’ar Allah Ya yi riko da hannayen sabbin shugabanni Ya kuma albarkaci kasar baki daya.