Sarkin Musulmi ya shawarci Buhari da Jonathan su amince da sakamakon zabe
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya shawarci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da babban abokin takararsa Janar Muhammadu Buhari, kan su amince da sakamakon zaben da za a gudanar a gobe Asabar. Sarkin Musulmin ya yi wannan kira ne a shekaranjiya Laraba a wata sanarwa da Babban Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam Dokta […]
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya shawarci Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da babban abokin takararsa Janar Muhammadu Buhari, kan su amince da sakamakon zaben da za a gudanar a gobe Asabar.
Sarkin Musulmin ya yi wannan kira ne a shekaranjiya Laraba a wata sanarwa da Babban Sakataren kungiyar Jama’atu Nasril Islam Dokta Khalid Abubakar Aliyu ya raba wa manema labarai a Kaduna. Ya ce yin haka ne zai tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kasar nan.
Sarkin Musulmin ya roki al’ummar Musulmi su ci gaba da yin addu’o’i don rokon Allah Ya sa a yi zaben cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.
“Muna rokon dukkan ’yan takarar, Shugaba Jonathan da Janar Buhari da wadanda ke takara a sauran jam’iyyu su amince da sakamakon zaben da za a yi da kyakkyawan nufi.
Tunda har Allah Ya sa za mu ga wannan zabe, akwai bukatar mu ga zabubbuka na gaba lafiya. Kada a rikita kasa har ta kai ga an lalata zaman lafiyar da muke da ita,” inji shi.
Ya ce duk wani ba daidai ba da aka yi a daure a mika ga kotu domin neman hakki kamar yadda ake yi a sauran kasasehn duniya. “Fatanmu ne a yi zabe mai ingance a kasar nan. Kuma muna fata Allah Ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a kasar nan,” inji Sarkin Musulmin.