Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram
Daga cikin ibadar da ake ƙarfafa wa Musulmi a cikinsa akwai Azumin Tashura ko Tasu’a da Ashura.
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’ummar Musulmi a Najeriya da su fara neman jinjirin watan Muharram, wanda shi ne watan farko a kalandar Musulunci.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Ba da Shawara kan Harkokin Addinin Musulunci na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya fitar a wannan Lahadin.
- Qatar ta samu makinta na farko a tarihin gasar Kofin Duniya
- Yau Lahadi za mu sanya hannu a yarjejeniya da Iran — Trump
Sanarwar ta ce an buƙaci Musulmi su fara duban watan daga yammacin ranar Litinin, 15 ga Yuni, 2026, wanda ya yi daidai da 29 ga Zulhijja, 1447AH.
Sanarwar ta buƙaci duk wanda ya hangi jinjirin watan da ya sanar da hakimi ko shugaban al’umma mafi kusa da shi, domin isar da rahoton ga Majalisar Sarkin Musulmi.
Watan Muharram na daga cikin watanni masu falala a Musulunci, kuma yana da muhimmanci ta fuskar ibadu da ladubba.
Daga cikin ayyukan ibadar da ake ƙarfafa wa Musulmi a cikinsa akwai azumin ranakun 9 da 10 ga watan Muharram, wato Azumin Tashura ko Tasu’a da Ashura.
A al’adance kuwa, Hausawa kan yi wa ranar 10 ga Muharram laƙabi da “Shara”, inda ake gudanar da wasu wasannin zumunci da al’adu tsakanin yara da manya.
Sai dai malamai da dama sun bayyana cewa wasu daga cikin waɗannan al’adu ba su da asali a koyarwar addinin Musulunci, don haka suke jan hankalin al’umma da su mayar da hankali kan ibadu da ayyukan alheri da Shari’a ta tanada a wannan wata mai albarka.