Sarkin Musulmi yana nan garau

Fadar Sarkin Musulmi ta ce zai halarci wani taro a Abuja, tana mai karyata jita-jitar rasuwarsa da ake yaɗawa.

Sarkin Musulmi yana nan garau

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar

Fadar Sarkin Musulmi ta karyata jita-jitar rasuwar Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad  Abubar III da ake yaɗawa.

Fadar ta yi Allah wadai da jita-jitar, tana mai bayyana cewa Mai Martaba Muhammad Sa’ad Abubakar yana cikin koshin lafiya.

Jami’in hulda da jama’a masarautar, Aminu Haliru ne ya sanar, yana mai bayyana cewa kowa ya san dukkan mutum zai mutu idan lokacin barin duniya ya zo.

Sa’in Kilgori  Dakta Muhammadu Jabbi Kilgori shi ya tabbatar Sarkin Musulmi na raye “Ba mu san mene ne suke son cimma wa da wannan jita-jitar ba, amma tabbas Sarkin Musulmi yana cikin koshin lafiya.

“Dazu ma muka bar jihar Kaduna domin halartar wani taro a Abuja kamar yadda ya saba.” 

Tun farko, shugaba kungiyar MPAC, Disu Kamor ya yi fatali da labarin da ake ta yaɗawa kan rasuwar Mai Martaba.

Kamor ya ce lafiyar Sarkin Musulmi garau babu abin da yake damun sa a halin yanzu, sannan ya gargadi al’umma da su guji yada jita-jita da kuma tantance labarin kafin fara yaɗawa.

Ta ce irin wadannan labarai marasa kan gado babu abin da za su kara illa rarrabuwar kawuna da kawo rudani