Sarkin Musulmi zai karrama Zakaran Gasar Musabaka ta Duniya

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar zai karrama Zakaran gasar Karatun Alkur’ani na Duniya Hafiz Kabiru Abubakar Musa wanda ya lashe gasar ta duniya karo na 35 da Gidauniyar Sarki Abdul Aziz na Saudiyya ke shiryawa da aka gudanar a Makka.Kabiru Musa wanda ya fito daga karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano, ya […]

Sarkin Musulmi zai karrama Zakaran Gasar Musabaka ta Duniya

LONDON, ENGLAND – FEBRUARY 18: The Sultan of Sokoto, Mohamed Sa’ad Abubakar waits to meet Prince Charles, the Prince of Wales at Clarence House on February 18, 2009 in London. The Sultan is the titular ruler of Sokoto in northern Nigeria. He is the leader of approximately 70 million Nigerian and West African Muslims and […]

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad AbubakarMai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar zai karrama Zakaran gasar Karatun Alkur’ani na Duniya Hafiz Kabiru Abubakar Musa wanda ya lashe gasar ta duniya karo na 35 da Gidauniyar Sarki Abdul Aziz na Saudiyya ke shiryawa da aka gudanar a Makka.
Kabiru Musa wanda ya fito daga karamar Hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano, ya zo na daya ne a gasar da mutum 150 daga kasashe 61 na duniya suka fafata wadda aka faro ta shekara 35 da suka gabata.
Shugaban Kwamitin Musabaka na Jihar Kano Alhaji Habibu Gwarzo ya shaida wa manema labarai a ranar Talata cewa Sarkin Musulmi ya ba da umanin cewa zakaran gasar ta duniya da sauran mahalarta gasar na isowa Najeriya su wuce Sakkwato domin shirya musu walimar girmamawa.
“Wannan shi ne karo na farko a shekara 20 da zakarar gasar a fagen hadda da tafsir ya fito daga Jihar Kano. Wannan abin farin ciki ne ga Jihar Kano da kuma Najeriya,” inji shi.
Shugaban ya gode wa Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da gwamnatin jihar da sauran masu ruwa da tsaki kan gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar gasar tun daga matakin kananan hukumomi zuwa jiha zuwa kasa zuwa ta duniya.
Kabiru Musa ya samu kyautar Riyal dubu 100 (kimanin Naira miliyan hudu), yayin da Mohammed Najm Abdul Kalam Azad daga Bangladesh ya samu kyautar Riyal dubu 80 (kimanin Naira miliyan uku da dubu 200) bayan da ya lashe gasar a mataki na biyu. Sai Abdul Kareem Abubakar ya samu Riyal dubu 60(kimanin Naira miliyan biyu da dubu 400), sai Ameen Mohammed Aftab Alam daga Saudiyya ya samu Riyal dubu 30 (kimanin Naira miliyan daya da dubu 200) da Khaled Mohammed Jobi daga Mauritius ya samu Riyal dubu 25 (kimanin Naira miliyan daya) wadanda suka zamo zakarun sauran ajujuwan gasar.
Wata sanarwa da ta fito daga Babban Mai taimaka wa Shugaban kasa kan Al’amuran Addini da Masallacin Fadar Shugaban kasa, Barista Tahir Umar Tahir ta ce Najeriya ta zo ta daya a babbar gasar ce bayan fafatawa da kasashe 60 na duniya, inda ya ce wannan ya nuna nasarar da sake fasalin kasa ke taka rawa a fannonin cin gaban kasa da harkokin addini.
Barista Tahir ya ce sakamakon kirkiro ofishin Manyan Masu Tallafa wa Shugaban kasa kan Harkokin Musulmi da na Kirista, Fadar Shugaban kasa ta tabbatar da cewa kasar Saudiyya ta sanya Najeriya a cikin gasar domin kauce wa maimaita lamarin da ya hana Najeriya shiga gasar a bara.