Sarkin Musulmin Kumasi ya karrama Zango da Nafisa Sai Wata Rana

Sarkin Musulmin Kumasi da ke kasar Ghana Omar Faroukh Sa’eed da kuma al’ummar kasar sun karrama fitattun jaruman fina-finan Hausa Adam A Zango da kuma Nafisa Abdullahi wadda aka fi sani da Nafisa Sai Wata Rana.An yi bikin karrama jaruman ne a fadar Sarkin Musulmin Kumasi. Wannan karramawar hadin gwiwa ce tsakanin Masarautar Kumasi da […]

Sarkin Musulmin Kumasi ya karrama Zango da Nafisa Sai Wata Rana

OLYMPUS DIGITAL CAMERA

Adam Zango ya ranqwafa a gaban Sarkin Kumasi na qasar Ghana Omar Faroukh a lokacin da sarkin yake karrama jaruminJarumi Majid Michel a lokacin bikin karrama Zango da NafisaSarkin Musulmin Kumasi da ke kasar Ghana Omar Faroukh Sa’eed da kuma al’ummar kasar sun karrama fitattun jaruman fina-finan Hausa Adam A Zango da kuma Nafisa Abdullahi wadda aka fi sani da Nafisa Sai Wata Rana.
An yi bikin karrama jaruman ne a fadar Sarkin Musulmin Kumasi. Wannan karramawar hadin gwiwa ce tsakanin Masarautar Kumasi da kamfanin shirya fim na Yahaleed Production da kuma kungiyar ‘yan fim ta Ghana mai suna ZAFMAG.
Sarkin ya ce an karrama Zango sakamakon fina-finan addini da yake yi wadanda suka fadakar da mutane yaya Musulunci yake, yaya kuma Musulunci yake daukar sauran addinai.
Su kuma al’ummar kasar Ghana sun karrama Zango da Nafisa ta hannun shahararren jarumin fina-finan Turanci Majid Michel da Abdulsalam Mumini da Papaa Angola a dandamalin taro na National Theatre da ke Accra babban birnin kasar Ghana a ranar 17 ga watan jiya.
A lokacin da Majid yake mika kyautar ga jaruman ne ya ce “mu al’ummar Ghana muna mika muku wannan kyautar ne bisa ga bisa kwazo da jajircewa da kuka yi wurin fitowa a fina-finan Hausa masu kayatarwa da nishadantarwa da kuma fadakarwa.”
Da wakilinmu ya tuntubi jarumin ne a kan karramawar da aka yi masa sai ya ce “Na yi matukar farin ciki sakamakon wannan karramawar. Ban taba samun kyauta a rayuwata mafi daraja kamar wannan ba. Don haka na yi alkawarin jajircewa da kuma zage damtse wurin samar da wakoki da kuma fina-finan da za su kara fadakar da mutane a kan addinin Musulunci.”
Ita ma Nafisa ta ce wannan karramawar za ta kara ba ta karfin gwiwa wurin ci gaba da yin fina-finan da za su fadakar da ’yan kallo.
A cikin wadanda suka yi wa jaruman rakiya akwai Abu Sarki da Darakta Falalu dorayi.
A yanzu dai jaruman sun dawo Najeriya don ci gaba da gudanar da harkokinsu.