Sarkin Qatar zai ziyarci Buhari a yau
A yau Talata sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Althani zai ziyarci shugaba Buhari a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja. Sarkin zai ziyarci shugaba Buhari ne bayan shekara uku da suka wuce Buhari ya ziyarci Doha babban birnin kasar Qatar a watan Fabrairun 2016 inda ya halarci taron Kungiyar kasashe masu fitar da danyen […]
A yau Talata sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Althani zai ziyarci shugaba Buhari a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja.
Sarkin zai ziyarci shugaba Buhari ne bayan shekara uku da suka wuce Buhari ya ziyarci Doha babban birnin kasar Qatar a watan Fabrairun 2016 inda ya halarci taron Kungiyar kasashe masu fitar da danyen man fetur ta OPEC.
Mai Bai wa Shugaban kasa Shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya sanar da hakan.