Sarkin Rano ya je ta’aziyyar Ɗan Isan Zazzau
Masarautar ta bayyana kaduwarta kan rasuwar basaraken.
Sarkin Rano, Alhaji Muhammad Isah Umaru, ya ya kai wa Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ziyarar ta’aziyyar rasuwar Ɗan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idris.
A ranar Lahadi, Sarkin Rano ya kai ziyara fadar Masarautar Zazzau da ke Zariya, inda ya bayyana alhininsa game da rasuwar basaraken.
- An kama matashi kan satar Al-Kur’anai a masallaci a Zariya
- NAJERIYA A YAU: Cire Tallafin Mai Ne Ya Jefa ’Yan Najeriya Cikin Kunci?
“Rasuwar Ɗan Isan Zazzau babban rashi ne, ba ga masarautar Zazzau kaɗai ba, har ga ɗaukacin masarautun Arewacin Najeriya. Allah Ya jiƙan sa da rahama, kumaYa bai wa iyalansa da Masarautar Zazzau haƙurin wannan rashi.”
Ya yi addu’a tare da nuna goyon baya ga masarautar da iyalan mamacin, ya kuma yi fatan Allah Ya ba su haƙurin rashinsa.
A martaninsa, Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya gode wa Sarkin Rano bisa ziyarar tasa.
Ya ce “Ko da yake muna cikin damuwa, mun amince cewa wannan ƙaddara ce daga Allah. Muna addu’a Allah Ya ba mu ƙarfin jure wannan jarabawa.”
Aminiya ta ruwaito yadda da Ɗan Isan Zazzau ya rasu a gidansa da ke Zariya a Jihar Kadun, ya rasu ya bar mata biyu da yara biyu.