Sarkin Rano ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji  Tafida Abubakar Ila II rasuwa. Marigayin ya rasu ne ranar Asabar a Asibitin Kwararru na Nasarawa da ke Kano da misalin karfe 4.45 na yamma bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya. A ranar Juma’a aka kwantar da marigayin a asibiti bayan ya yi fama […]

Sarkin Rano ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya

Marigayi Sarkin Rano, Dokta Tafida Abubakar Ila

Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji  Tafida Abubakar Ila II rasuwa.

Marigayin ya rasu ne ranar Asabar a Asibitin Kwararru na Nasarawa da ke Kano da misalin karfe 4.45 na yamma bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

A ranar Juma’a aka kwantar da marigayin a asibiti bayan ya yi fama da ciwon da zuwa yanzu ba a tatance shi ba.

Turakin Rano Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya tabbatar wa Aminiya rasuwar.

Honorebul Alhassan Rurum, wanda tsohon shugaban majalisar jihar Kano ne, ya bayyana cewa za a yi jana’izar Sarkin da yammacin  Asabar kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Kafin rasuwarsa, shi ne Sarkin Rano na farko bayan da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kirkiri karin masarautu hudu daga masarautar Kano.

Ma’aikatan Abuja ba sa sona — Wike

Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda

Mutane Biyu Sun Mutu, Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Ruwan Sama A Gashuwa

Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro

Tags