Sarkin Ringim ya hori jama’a su yi koyi da Majiya
Mai martaba Sarkin Ringim Alhaji Sayyadi Mahamood Abubakar ya shawarci masu hannu da shuni da ke masarautarsa da Jihar Jigawa da Najeriya su yi koyi da kyawawan halaye na taimakon jama’a irin na Adamu Musa Majiya, musamman yunkurinsa na kafa jami’a mai zaman kanta a masarautar. Sarkin ya fadi haka ne a fadarsa a ranar […]
Mai martaba Sarkin Ringim Alhaji Sayyadi Mahamood Abubakar ya shawarci masu hannu da shuni da ke masarautarsa da Jihar Jigawa da Najeriya su yi koyi da kyawawan halaye na taimakon jama’a irin na Adamu Musa Majiya, musamman yunkurinsa na kafa jami’a mai zaman kanta a masarautar.
Sarkin ya fadi haka ne a fadarsa a ranar Talata da ta gabata lokacin da wakilan Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) da ’yan kwamitin gina Jami’ar Khadija suka kai masa ziyarar ban-girma a fadarsa.
Alhaji Sayyadi Mahamood ya ce wannan jami’a ita ce ta farko a Jihar Jigawa a matsayin jami’a mai zaman kanta kuma ya zama dole a jinjina wa wanda ya yi kokarin samar da ita domin gina jami’a ba karamin aiki ba ne.
Sarkin ya bukaci wanda yake kokarin gina jami’ar ya kai ziyarar ban-girma ga fadar Mai martaba Sarkin Kano, domin neman shawarwari, inda ya ce yana da masaniyar Sarkin zai taimaka da shawarwari.
Ya ce gina jami’ar zai taimaka wajen daukar dalibai masu sha’awar karatu a jihar da kuma makwabta.
A jawabin, jagoran ayarin Farfesa Sagir Adamu cewa ya yi sun zo fadar ce don neman albarka.