Sarkin Saminaka ya nada Limamin juma’a na Mangwarori Saminaka
Mai martaba Sarkin Saminaka dake Jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada Malam Shu’aibu Mai Kwalli a matsayin Limamin sabon masallacin juma’a na Mangwarori dake garin Saminaka da Malam Isah Alhassan a matsayin Na’ibi na daya da kuma Malam Hamisu Adamu Kadade a matsayin Na’ibi na biyu a fadarsa dake garin Saminaka. Da yake […]
Mai martaba Sarkin Saminaka dake Jihar Kaduna, Alhaji Musa Muhammad Sani ya nada Malam Shu’aibu Mai Kwalli a matsayin Limamin sabon masallacin juma’a na Mangwarori dake garin Saminaka da Malam Isah Alhassan a matsayin Na’ibi na daya da kuma Malam Hamisu Adamu Kadade a matsayin Na’ibi na biyu a fadarsa dake garin Saminaka.
Da yake jawabi a lokacin Mai martaba Sarkin na Saminaka ya mika godiyarsa ga al’ummar yankin kan irin goyan baya da hadin kan da suka bashi wajen nada Limamin tare da na’ibansa.
Ya ce sun yi wannan nadi ne badan muci zarafin kowa, ko don a kawo rarrabu a tsakanin al’umma ne ba. An yi nadin ne domin a zauna lafiya, kuma a karfafa addinin musulunci.
Ya ce babu shakka wannan nadi zai kara donkon zumunci a tsakanin al’ummar yankin.
Ya yi kira ga limamin da na’iban su sani cewa an basu amana ce kan wannan nadi da aka yi masu. Don haka ya yi kira kan su tashi tsaye wajen daukaka addinin musulunci, a wannan masallaci. Kuma su cigaba dayin addu’o’in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da cigaba a wannan yanki.
A nasa jawabin Limamin sabon Masallacin juma’a na mangwarori Saminaka Malam Shu’aibu Mai Kwalli ya mika godiyarsa ga Allah da mai martaba Sarkin Saminaka da Turakin Saminaka Alhaji Ado Abubakar Yango da dukkan al’ummar yankin kan goyan bayan da suka bashi wajen ganin an yi masa wannan nadi.
Daga nan ya yi addu’ar Allah Ya zaunar da kasar nan lafiya.