Sarkin Saminaka ya nemi makarantu masu zaman su sassauta kudin makaranta

Mai martaba Sarkin Saminaka a Jihar Kaduna Alhaji Musa Muhammad Sani ya bukaci makarantu masu zaman kansu su rika sassauta kudin da suke karba daga wajen iyayen yara. Sarkin ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a wajen yaye daliban makarantar Saminaka Academy da ke Saminaka, inda ya ce yin wannan kira […]

Sarkin Saminaka ya nemi makarantu masu zaman su sassauta kudin makaranta
Sarkin Saminaka ya nemi makarantu masu zaman su sassauta kudin makaranta

Mai martaba Sarkin Saminaka a Jihar Kaduna Alhaji Musa Muhammad Sani ya bukaci makarantu masu zaman kansu su rika sassauta kudin da suke karba daga wajen iyayen yara.
Sarkin ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a wajen yaye daliban makarantar Saminaka Academy da ke Saminaka, inda ya ce yin wannan kira ya zama wajibi, idan aka dubi irin makudan kudi da wasu makarantu masu zaman kansu suke karba daga iyayen yara. Ya ce ya kamata masu makarantun su dubi irin halin da ake ciki a kasar nan, na rashin kudi.
Ya yaba wa wanda ya gina makarantar Saminaka Academy, inda ya ce ya ba da gagarumar gudunmawa wajen ilimintar da matasan yanki ta hanyar gina makarantar. Ya yi kira ga masu hannu da shuni a yankin su yi koyi da shi don bayar da tasu gudunmawa wajen bunkasa yankin.
A jawabin Hakimin Tama da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Alhaji Adamu Yakubu Tama ya ce samun irin mai makarantar a cikin al’umma ci gaba bane domin da haka ne ake samu a gina matasa su zama nagari.
Ya yi kira kan a bude sashin kwana a makarantar, don daliban da suke nesa su samu shiga makarantar.
A jawabin wanda ya gina makarantar Alhaji Bala Yunusa Dini ya ce ya bude makarantar ce ba da gudunmawarsa wajen ilimintar da yaran yankin musamman ’ya’yan talakawa.
Ya ce sun fara da dalibai 50 a shekara ta 2005, amma a yanzu suna da dalibai sama da 600 a sashin firamare da sakandire.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi